Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Tsegumi da gaske ne an wanke mawaki Rarara?


Tsegumi da gaske ne an wanke mawaki Rarara?

Daga Idris Umar, Zariya

Jami’ar European American University ta musanta bai wa fitaccen mawaʙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, digirin girmamawa na dokta.

A jiya Asabar ce dai wani bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta ya nuna yadda ake karrama Rarara da digirin girmamawa a wani bikin yaye ɗalibai da aka gudanar a otel ɗin NICON Luxury da ke Abuja.

Sai dai cikin wani saʙo da ta fitar a shafinta a ranar Asabar, jami’ar ta ce sam ba ta da hannu a lamarin kuma ba da izininta ba.

Jami’ar ta bayyana cewa, ba ta taɓa ba da izinin gudanar da taron karramawa ko taron yaye ɗalibai a wannan wurin da kuma wannan ranar ba.

Sanarwar ta ʙara da cewa, an shirya taron ne ta hanyar yaudara, ba tare da sanin jami’ar ba kuma ba tare da amincewarta ba.

Haka kuma, ta ce waɗanda suka shirya taron, sun yaudari jama’a “da nuna kamar suna wakiltar Jami’ar European-American.

“Wannan kuwa ʙarya ce tsagwaronta, domin ba su da wata alfarma ko izini, balle kuma su karɓi kuɗi a madadin jami’ar.

Jami’ar European-American ta ʙara da cewa, “ba ta taɓa bai wa Dauda Kahutu Rarara, Alhaji Ahmed Saleh Jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa ko Tarela Boroh wata girmamawar digirin Doktora ba.

“Dukkan waɗanda jami’ar ta karrama da digiri na gaskiya suna cikin rajistar dalibai da aka yaye wacce ake iya dubawa a hukumance.”

Tun bayan ɓullar labarin digirin girmamawa da aka yi wa fitaccen mawaʙin siyasar, mutane da dama suke tofa albarkacin bakinsu, inda da dama suka taya shi murna, a ɓangare guda kuma wasu suka ʙalubanci lamarin.

Post a Comment

0 Comments