An Kama Editan Jarida Learship Hausa online Saboda Zargin Fallasa wata yarjejeniyar kuɗi Naira Miliyan 30 a Zariya zuwa Katsina
Daga Idris Umar,Zariya
Rahoton dake shigo mana da safiyar nan daga Zaria, Jihar Kaduna ya bayyana yadda jami’an ’yan sanda sun kama wani ɗan jarida na Hausa, Editan Leadership Hausa Online News da Albishir Hausa Newspaper, wato Zuhair Ali Ibraheem, bisa umarnin wanda rahoton ya shafa.
Majiyoyin al’umma sun bayyana cewa, an kama Ibraheem ne bayan ya wallafa labarin bashin da ya shafi kansilar, bayan ya saurari bangarorin biyu. Zarge-zargen sun nuna cewa, Kansilar Nuhu ya karɓi bashi na Naira miliyan 30 daga wajen Alhaji Ibrahim Bindawa, inda ya yi ikirarin cewa kuɗin “aikin musamman za'a yi ma Gwamna Dr. Dikko Umar Radda
Sai dai, Kansilar ya kasa biyan bashin, sannan ana zarginsa da yin barazana ga Alhaji Bindawa, inda yake ikirarin cewa matsayin sa na zababben Kansila ba wanda ya isa ya raina shi.
Kamar yadda Jaridar da yake aiki ta leadership Hausa online suka wallafa a Shafinsu a yanzu.
Ya zuwa haɗa wannan rahoto she editan na hannun hukuma don gudanar da cikakken bincike.
0 Comments