Tsarabar mu ta yau
Ba Rabo Da Gwani Ba Shekaru 35 A Radio Nijeriya Kaduna
Daga Ibrahim Idris Kaura-Namoda
A Ranar 20 ga Watan Satumban 1990 Habibu Tabari yafara aiki da Radio Nigeria Kaduna Shekaru 35 kenan da Suka gabata inda yafara aiki a Matsayin karamin Ma’aikaci a Sashen Sirye Shirye.
Habibu Tabari ya gabatar da Shirye Shirye da Suka hada da gabatar da Zabe,Shirin Filin ‘Yan Club,Filin wasa Kwakwalwa da Shirye Shirye addinin musulunci kamar Shirin Rabin Sa’ar Makarantar Sheikh Abubakar Gummi,
Shirye Shirye Hajjin Bana da Tafsiran Alqur’ani Mai Girma da dai sauran Shirye Shirye. Saidai Shirin da Habibu Tabari yayi fice a Radio Nigeria Kaduna shine Shirin Jakar Magori da a shekarun baya yayi Suna a matsayin Dan Autan Jakar Magori kasantuwarshi na karami a Shekaru cikin Masu kawo rahotanni a Shirin Wanda daga bisani yazamo Madugu Kuma Jagoran Shirin har lokacin da yazamo Mai kula da Shirin Jakar Magori dama sauran Shirye Shirye.
Habibu Tabari ya halarci kwasakwassai a Kwalejin horas da Ma’aikatan Radio ta Radio Nigeria dake Ikeja a Birnin Ikko dama kwasa kwassai da dama.
Habibu Tabari kwararren ma’aikacin Radio ne da Kuma yakoyar da nakasa dashi dama koyar da dayawan Dalibbai Masu neman sanin makamar aiki dama masuyiwa Kasa hidima.
Sanin aikin Radio da Kwarewar Habibu Tabari yasa a Ranar Ranar 30 ga Watan Ugastan wannan shekara ta 2025 Kungiyar Ma’aikatan Radio da Talabiji da Masu wasan kwaikwayo reshen Radio Nigeria Kaduna karrama Habibu Tabari a matsayin Gwarzon shekara wajen Shirya Shirye Shirye bayaga wasu karramawar da yasamu a shekarun baya.
A wannan Rana ta 20 ga Watan Satumban 2025 Habibu Tabari ya cika Shekaru 35 a matsayin ma’aikacin Radio Nigeria Kaduna Ranar da aikinshi yazo karshe.
Sashen Sirye Shirye dama Radio Nigeria Kaduna hada da masu sauraren Radio Nigeria Kaduna zasuyi kewar Muryar Habibu Tabari saidai Ilmin da yabari za’a cigaba da amfana
0 Comments