Bayar da hutun Maulidi a ƙaramar hukumar Sabon Gari: An yabawa Hon. Albani Samaru
Daga Idris Umar, Zariya
A taron Maulidi da ya gudana a ranar Laraba 24/9/2025, malamai da dama sun yabawa shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Hon. Abubakar Jamilu Albani Samaru, bisa bayar da hutun kwana ɗaya ga jama'ar ƙaramar hukumarsa don gudanar da bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Kungiyar Fitiyanul Islam ta ƙasa reshen ƙaramar hukumar Sabon Gari, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sharu Dallami Zariya, ce ta shirya gagarumin taron Maulidi a babban masallacin Kwata da ke Sabon Gari, Zariya.
Taron ya samu karɓuwa daga bangarori daban-daban – malamai, sarakuna, da 'yan siyasa na ƙaramar hukumar Sabon Gari da wajenta.
Bayan an gudanar da wa'azi kan darajojin Annabi (SAW), da malamai da dama suka gabatar ciki har da Sheikh Surajo Bomo, sai shugaban taron, Sheikh Sharu Dallami, ya gabatar da jawabin godiya da jinjina ga shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari da wakilinsa Hon. Kamilu, da dukkan 'yan majalisar dokokin ƙaramar hukumar Sabon Gari da suka halarci taron don wakiltar shugaban ƙaramar hukumar Hon. Abubakar Jamilu Albani.
Sheikh Sharu Dallami ya jinjina wa Hon. Abubakar Jamilu Albani bisa cika alkawarin da ya ɗauka a wasu lokuta a baya inda ya ce, in har ya ci zaɓen kujerar da yake nema, to zai bayar da rana guda ɗaya a matsayin hutu don gudanar da bukukuwan Maulidin Annabi Muhammad (SAW) ga masu gudanarwa a fadin ƙaramar hukumar Sabon Gari a hukumance.
Bisa haka, shaihin malamin ya jagoranci yin addu'a ta musamman ga shugaban ƙaramar hukumar da mataimakinsa da majalisar dokokin ƙaramar hukumar, don neman Allah ya ƙara ba su nasara a dukkan manufofinsu na alheri.
Daga ƙarshe, Hon. Kamilu ya gabatar da jawabi a madadin shugaban ƙaramar hukumar ta Sabon Gari game da hutun kwana ɗaya da gwamnatin ƙaramar hukumar ta bayar. Ya kuma amsa tambayoyin manema labarai a kan zarge-zargen da wasu ke yi wa shugabancin ƙaramar hukumar cewa gwamnatin tana nuna son kai da ɓangaranci wajen bayar da muƙamai.
Tuni Hon. Kamilu ya ƙaryata zarge-zargen a bainin jama’a ga manema labarai.
Hon. Kamilu ya ce, kowa ya sani cewa shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Honorabul Abubakar Jamilu Albani, ɗan ƙungiyar Izalatul-Bidi’a ne, amma bai taɓa nuna ƙyama ba ga wasu ɓangarorin mutanen da yake tare da su a kujerar shugabancin ƙaramar hukumar tun farko har yanzu.
Hon. Kamilu ya ƙara da cewa, shi kansa a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, ba ɗan Izala ba ne ɗan Darikar Tijjaniyya ne kuma babu wata matsala a tsakaninsu da mabiya darikar Izala, domin tare suke gudanar da komai lafiya.
A ƙarshe, Hon. Kamilu ya yabawa shugaban nasa bisa alkawarin da ya cika na bayar da hutun kwana ɗaya don gudanar da bukukuwan Maulidi a fadin ƙaramar hukumar Sabon Gari. Ya ce suna alfahari da wannan ƙoƙari nasa, sannan ya gode masa bisa irin wannan namijin ƙoƙari.
Malamai da dama sun yi jinjina ga shugaban yayin da suke gabatar da wa'azinsu a wajen. Cikinsu akwai Sheikh Surajo Bomo Zariya da Sheikh Suleman Limanci da Honorabul Sani Bazawa daman majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar Basawa duk sun nuna jin daɗinsu tare da fatan alheri ga shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Hon. Abubakar Jamilu Albani Samaru.
An yi taro lafiya, an tashi lafiya.
0 Comments