HON. AHMED MUNIR YA KARA JADDA RAWARSA WAJEN TALLAFAWA SHIRIN SUSTAIN NA GWAMNAN JIHAR KADUNA, SANATA UBA SANI
Kaduna, Najeriya – 23 ga Satumba, 2025
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Lere, Hon. Ahmed Munir, ya jaddada cikakken goyon bayansa ga Shirin SUSTAIN na Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tare da alƙawarin mara masa baya domin nasarar tazarce a wa’adin mulki na biyu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Daraktan Gabaɗaya na UBA WIN PROJECT, Hon. Mukhtar Zubairu (Sadaukin Hayin Dogo), ƙungiyar da ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Sanata Uba Sani a zaben 2023, wacce kuma ke ci gaba da jagorantar aikin wayar da kan jama’a domin tabbatar da nasarar sake zaben sa.
A jawabinsa, Hon. Munir ya ce: “Shirin SUSTAIN ba kawai taken siyasa ba ne; tsari ne na gaskiya da ke canza rayuwa a fadin Jihar Kaduna. Ina nan daram wajen tallafawa wannan tsari tare da tabbatar da nasarar Mai Girma Gwamna a wa’adin mulki na gaba.”
Shirin SUSTAIN yana nufin: Tsaro da Kare Lafiya, Haɗin Kai, Cigaban Gine-gine, Gaskiya da Bayyananniyar Mulki, Inganta Noma, Bunkasa Masana’antu, da Gina Ɗan Adam.
Hon. Munir ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da haɗa kai domin dorewar ci gaba da zaman lafiya a Kaduna.
0 Comments