Shugabannin Kungiyar Fulani ta Jihar Kaduna Sun Kai Ziyara Ga Shugaban Kungiyarsu na Kasa
Daga Idris Umar Zariya
A ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2025, shugabannin kungiyar Fulani ta jihar Kaduna, Miyetti Allah Kautal Hore, karkashin jagorancin sabon shugaban su na jiha, Alhaji Aminu Jibirin, sun kai ziyara ta musamman ga shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello, a Anguwar Maliya, karamar hukumar Kauru, jihar Nasarawa.
Ziyarar, wadda aka shirya domin karfafa zumunci da hada kan al'ummar Fulani a fadin kasa, ta samu halartar shugabannin Fulani daga dukkan kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
A yayin taron, an gabatar da jawabai masu muhimmanci da suka shafi ci gaban al’ummar Fulani da kuma rahotanni daga wakilai game da halin da Fulani ke ciki a matakin jiha da na kasa. Wannan ya karawa shugabanni da sarakunan gargajiya kwarin gwiwa don ci gaba da ba da gudunmawa wajen kare muradun Fulani a Najeriya.
Shugaban kasa na kungiyar, Alhaji Bello, ya yaba da irin kokarin da sabon shugaban na jihar Kaduna ke yi, tare da yin kira ga sauran kungiyoyin Fulani da su mara masa baya domin ci gaban al'ummar Fulani gaba daya. Ya kuma jinjina wa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa tsarin da ya ke shimfida na zaman lafiya a fadin jihar.
Shugaban ya kuma ja hankalin daukacin membobin kungiyar da su zama jakadu na zaman lafiya da hadin kai, yana mai tabbatar da cewa da ikon Allah, za a samu tabbataccen zaman lafiya a Najeriya.
A nasa jawabin, Alhaji Aminu Jibirin ya nuna godiya ga shugaban kasa na kungiyar bisa tarbar da ya musu, tare da bayyana kudirinsa na tabbatar da adalci da ci gaba a tsakanin mambobin kungiyar a jihar Kaduna. Ya kuma tabbatar da cewa za su yi duk mai yiwuwa domin hada kan Fulani a cikin kananan hukumomi 32 da ke fadin jihar.
Alhaji Aminu ya gode wa sarakunan gargajiya da sauran dattawan da suka mara musu baya, tare da yin addu’a ga cigaban kungiyar da zaman lafiya mai dorewa a jihar da kasa baki daya.
Daga cikin manyan baki da suka halarci wannan ziyara akwai:
Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Sani Ibrahim
Sarkin Kauru, Alhaji Abubakar
Alhaji Gidado Sadik Bebeji, daya daga cikin fitattun dattawan kungiyar.
0 Comments