Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi.
Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.
A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.
A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.
Ya kuma yi kira ga Æ´an siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.
Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.
0 Comments