Header Ads Widget

Responsive Advertisement

kungiyar manoman asali ta Arewa ta koka kan yadda ake nuna mata Yan'Ubanci


kungiyar manoman asali ta Arewa ta koka kan yadda ake nuna mata Yan'Ubanci

Daga Idris Umar, Zariya

Kungiyar manoman asali  ta Arewa, ta koka da yadda ake fifita kayan hatsi na Kasashen ketare a maimakon na gida.

Kungiyar ta muna matukar damuwa tare da yin Kiran don yiwa tubkar don maido da martabar noma a Najeriya*


Kungiyar manoman asali  ta Arewa (Arewa Grassroots Famers Alliance of Nigeria) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta fifita sayen hatsi na gida a maimakon wadanda   ake shigowa da su daga kasashen waje.

 Kantoman riko na kungiyar, Comrade Dauda Musa Namadi, ya yi  wannan Kiran a lokacin wani taron da kungiyar ta shirya a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.

 Comrade Dauda,  ya ce,  kamata ya yi Gwamnati ta fifita sayen hatsi na gida don kara inganta samarwa da bunkasa tattalin arziki manoma.

" Gwamnati za ta tabbatar da wadatar abinci ga jama'a ne  muddin ta  bunkasa  amfani da hatsin cikin gida da rage yawan dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje" ---- a cewar shugaban kungiyar manoman.

Kwamrade Dauda ya  jaddada cewar Gwamnati, ya kyautatu ta rika sayen amfanin gona da manoman ainihi na gida ke Samarwa ta karyar dasu a farashi mai sauki  don saidawa  jama'a ko kamfanoni, in kuma ba ta iya sayen kayayyakin amfanin gona da manoman asali Ke nomawa don tallafawa manoman da suke kashe makudan kudade wajen harkokin noman,  to ta daina barin ana shigo dana Kasashen ketare, don kayayyakin  cikin gida su yi gogayya da sauran kayan hatsi na Kasashen waje.

Shugaban kungiyar manoman asalin Comrade Dauda, ya Kara da cewa duk da muhimmancin Noma ga ci gaban Kasa, manoman kasarnan da dama na fuskantar ʙalubale tun daga Kan rashin tsaro da rashin fifita abun da suke nomawa, wanda hakan  ya Zama barazana ga harkokin noman manoman dake taimawa wajen samar da abinci mai tarin yawa ga alummar Najeriya don haka  ba za su lamunci wannan lamarin ba, sai  ya yi Kira ga gwamnatin ta dauki kwararan matakan dakile haka Ko su Shiga yajin aiki.

Wasu daga cikin manoman kungiyar Ashiru Tanko Makarfi da Alhaji Shehu Ibrahim da sauran manoman da suka halarci taron da suka tofa albarkacin bakinsu, sun nuna rashin jindadinsu da Yadda ba a la'akari da wahalhalun da suke fuskanta na noma sai rika  tsallakewa ana shigowa da wasu Kayan hatsi daga waje, daga nan sai suka bukaci masu ruwa da tsaki su yi wa tubkar hanci.

Kungiyar manoman asali  ta Arewa (Arewa Grassroots Famers Alliance of Nigeria, ta ce za ta Ci gaba da yin irin wadannan kiraye kiraye har sai gwamnati ta shawo Kan lamarin dake Neman fin karfin kundila.

Post a Comment

0 Comments