Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari ya Sake bai wa Dalibai tallafin karatu (Kashi na 4)

Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari ya Sake bai wa Dalibai tallafin karatu (Kashi na 4)

Daga Idris Umar Zariya

Shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru (ALGON), ya ci gaba da raba tallafin karatu ga É—alibai a karamar hukumar, inda yanzu haka ya bai wa É—alibai kusan 100 tallafi a zagaye na huÉ—u na shirin.

Wannan tallafi na daga cikin hanyoyin da shugaban ke amfani da su domin Æ™arfafa ilimi a karamar hukumar. An gudanar da taron kaddamar da shirine a bubban dakin taro dake harabar sakatariyar dake Dogarawa  inda mataimakin shugaban karamar hukumar, Honorabul Abdulkareem Kamilu, ya wakilci shugaban wajen gabatar da tallafin. A jawabin sa, ya yaba da irin yadda shugaban ke kokari, ya ce suna ganin abin kunya ne idan suka kasa aiki da gaskiya ganin irin jagorancin da suke samu daga sama.

Ya kara da cewa, manufarsu shi ne su ga cewa matasa sun samu ilimi saboda wanda ka ba shi ilimi kamar ka ba shi duniya ne baki É—aya.

 Ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani saboda goyon bayan da yake ba su a fannin ilimi da sauran ayyuka.

Ya roki É—aliban da suka samu tallafin su yi amfani da damar ta hanya madaidaiciya domin amfaninsu da na al’umma gaba É—aya.

Haka zalika, Dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar Basawa, Hon. Sani Bazawa, shi ma ya bayyana farin cikinsa da wannan tallafi. Ya ce irin wannan kokari na nuna yadda shugabannin ƙananan hukumomi ke ɗaukar ilimi da muhimmanci. Ya kuma jinjina wa gwamna bisa goyon bayan da yake bayarwa.

Sakataren kwamitin ilimi na karamar hukumar Sabon Gari, wanda ya zanta da manema labarai bayan taron, ya bayyana cewa duk É—aliban da suka sami tallafin sun bi matakan da suka dace kuma sun cika dukkan sharuddan da aka tsara. Ya kuma yabawa shugaban bisa yadda yake nuna kulawa da fannin ilimi.

Daga cikin waÉ—anda suka amfana da tallafin, akwai wani É—alibi da ya bayyana farin cikinsa da godiya ga shugaban karamar hukumar, yana mai fatan Allah ya saka masa da alheri.

Fatima, wata ɗaliba da ta ci gajiyar tallafin, ta bayyana cewa tana farin ciki matuƙa da irin wannan tallafi, musamman ganin yadda aka yi adalci.

 Ta yi addu’ar fatan alheri ga Honorabul Albani, tana fatan Allah ya taimake shi a rayuwa duniya da lahira.

Bayan kammala taron, daliban da suka sami tallafin sun yi waka da sallama ga Gwamna Uba Sani, suna masa fatan alheri da rayuwa mai amfani.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments