Tsarabarmu ta yau
Daga Idris Umar, Zariya
Wannan tsarabace daga abokan zumuncinmu da fatan kaima kuma zaku turo mana naku tsarabar ta koment secshon musha karatu lafiya.
Watarana na fito ƙofan gida sai naga mutane sun cika a ƙofan gidan dukda cewa dama wajene da yake tara mutane sosai, saboda ƙofan gidan mu akwai mahauta sosai (masu saida nama).
Bayan nazo na zauna cikinsu to daga gefe akwai wani wanzami yana yiwa wani Aski, to bayan ya gama masa Aski sai naga ya tara dukkan Gashi daya Askewa wannan mutumin ya tara wuri guda, saiya ƙira wata fullo mai nono (ma'ana mai sayar da nono) saiyace mata yanason nono, bayan ya sayi nonon saiya zuba suga. Nidai ina gefe ina kallonsa, sai naga ya ɗebo wannan Gashin daya tara waje guda ɗin, sai naga ya zuba cikin wannan nonon ya gauraya.
Bayan ya gauraya sai naga ya ɗaga yana sha. Subhan Allah. Abun yabani mamaki sosai, amma dake muna magana dashi sosai saboda yana aikana kuma ƙofan gidan mune, mun saba, saina tambayeshi, nace masa baka tunanin Gashin zai cutar dakai? Sai yayi Murmushi yace Bilal ai kaine kake kallo kamar nine nasha, ai ba'a cikina na saka ba.
Sai nace masa to a cikin wayene ka saka?
Sai yace, wallahi aikin kuÉ—i nayi yanzu haka, a cikin wani mutum ne nasaka, Inna lillahi wa'inna ilaihir.
Bayan naji tsoron maganar na gudu, saina tambayi wani mahauci, shin da gaskene abunda wannan wanzamin ya faÉ—a? Saiyace eh wallahi da gaskene, daga baya still na tambayi mahaifina saiyace ai haka suke mugayen mutane ne, sai nacewa babanmu wallahi ina kallo yasha gashi da nono, sai babana yacemin na daina faÉ—a kar nima yayimin mugunta.
Dalilin da yasa na bada wannan labarin shine, daga baya naji wanda ya sashi wannan aikin, kwanaki kuma sainaji shima ya rasu. To ina amfanin cutar da wani tunda bazaka iya kare kanka daga mutuwa ba? Tabbas duniya abun tsorone, kuma É—an Adam abun tsorone, Allah ya rabamu da shirka, Sihiri, tsafi, Ameen.
0 Comments