Ina kira da a saki dan jarida da aka kama a bakin aikinsa a garin Abuja – Kwamred Umar Samaru
Daga Fatima Idris Zariya
Ga sakon Kwamred Umar Idris game da kama Dan jarida da hukuma tayi a garin Abuja yace, "Ni, Kwamred Umar Idris Samaru, ina kira da gaggawa ga gwamnatin tarayya da kuma hukumar ‘yan sanda da su saki dan jarida Malam Nasir Yelwa, wanda jami’an tsaro suka kama yau a yayin da yake bakin aikinsa, yana daukar rahoto kan zagayen Maulidin Manzon Allah (SAW) da mabiya darikar Shi’a suka shirya a garin Abuja.
Ina tambaya: menene laifinsa? Me ya aikata? Daukar rahoton Maulidi ne laifi yanzu? Wannan abin da aka yi masa cin zarafi ne, keta haddin dan jarida ne, kuma zalunci ne karara. Dole ne mu tashi tsaye mu kare ‘yancin ‘yan jarida a Najeriya.
Muna kira da a saki Malam Nasir Yelwa ba tare da wani sharadi ba. Wannan al’amari yana nuna yadda jami’an tsaro ke ci gaba da tauye hakkin ‘yan jarida a kasar nan, musamman lokacin da suke bakin aiki. Wannan ba karamin koma baya bane ga ‘yancin fadar albarkacin baki da aikin jarida a Najeriya.
Haka kuma, ina kira ga shugabannin kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida su tashi tsaye, su dauki matakin gaggawa kan wannan lamari da makamantansa.
Ina kuma shawartar ‘yan uwana ‘yan jarida da mu rika bin dokoki da ka’idojin aiki lokacin da muke fita domin gudanar da ayyukanmu. Dole ne mu tabbatar da cewa akwai kyakkyawar fahimta da hadin kai tsakaninmu da jami’an tsaro, domin aikinmu daya ne – wato kare jama’a da kuma bayyanawa al’umma gaskiya.
A karshe, ina addu’a da fatan samun zaman lafiya a Najeriya baki daya, tare da fatan ganin cewa irin wannan cin zarafi bai sake faruwa ba a nan gaba.
0 Comments