Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari ya ɗauki nauyin ɗalibai 69 domin inganta rayuwar su


Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari ya ɗauki nauyin ɗalibai 69 domin inganta rayuwar su

Daga A'isha Suleman, Zariya 

Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Honorabul Jamilu Abubakar Albani ya ɗauki nauyin ɗalibai marayu da marasa ƙarfi 69 domin inganta rayuwar su a makarantar Al-Makkah Academy. 

Shugaban ƙaramar Hukumar wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar ƙananan hukumomin na jihar Kaduna, ALGON ya shaida cewa a koyaushe suna duba marayu da marasa ƙarfi domin ganin sun tallafawa rayuwarsu. 

Shugaban wanda dama ya saba bayar da irin wannan gudunmawa, wanda ko a kwanakin baya ya tallafawa ɗaliban Sakandare da kuɗin rubuta jarabawar hukumar WAEC da NECO, kazalika da bayar da tallafi ga ɗaliban gaba da Sakandare, ya jaddada aniyarsa na ci gaba da zaƙulo irin waɗannan nau'i na mutane domin tallafa musu ta fuskar ilimi da sana'o'in dogaro da kai. 

Ɗaliban da suka amfana da wannan tallafi a yayin tattaunawarsu da wakilinmu, sun miƙa godiyarsu ga shugaban ƙaramar Hukumar, tare da yi masa addu'ar fatan alheri. 

Kazalika al'ummar garin Samaru da kewayenta sun miƙa godiyarsu ga ALGON kuma shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru bisa wannan taimako da ya yi na ɗaukar nauyin karatun na marayu da 'ya'yan marasa ƙarfi; "mun gode, Allah ya saka da alheri", in ji ɗaya daga cikin al'ummar Samaru.

Post a Comment

0 Comments