Header Ads Widget

Responsive Advertisement

IAR Ta Nuna Sabbin Fasahohin Noma a Taron Shekara 2025 a Zariya

IAR Ta Nuna Sabbin Fasahohin Noma a Taron Shekara 2025 a Zariya 

Daga Idris Umar Zaria

 Cibiyar Binciken Noma (IAR) da ke Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta gudanar da bikin Farm Walk na shekara ta 2025 a ranar Alhamis, a gonar binciken IAR da ke Samaru.

Taron ya samu mahalarta daga sassa daban-daban, ciki har da masana kimiyyar noma da dalibai, da masu ruwa da tsaki a harkar noma daga cibiyoyi daban daban

Babban bako a taron shi ne Mataimakin Shugaban Jami’a (Mai kula da Ci gaban Jami’a, a ɓagaren Bincike da Kirkire-Kirkire), Farfesa Sunusi Rafindadi, wanda ya wakilci Shugaban Jami’a, Farfesa Adamu Ahmed A jawabinsa na bude taro, Farfesa Rafindaɗi ya yabawa IAR bisa jajircewarta wajen ci gaban binciken noma, kirkire-kirkire da yaɗa sabbin fasahohin da suka dace da bukatun Najeriya da ma ƙasashen waje.
Cikin jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Daraktan IAR, Farfesa Ado Yusuf, wanda Farfesa Nafiu Abdu ya wakilta, ya jagoranci manyan baki zagayen filayen bincike da kayayyakin aikin cibiyar.

Ya bayyana wasu daga cikin manyan nasarori da aka samu a ƙarkashin jagorancinsa, kamar su:

Kammala katanga (shinge) a gonar kayan lambu

Inganta gine-gine da ababen more rayuwa a gonar bincike

Kara karfin gudanar da gwaje-gwajen iri da sabbin fasahohi
A yayin zagayen, an nuna a zahiri yadda sabbin nau'ikan amfanin gona ke yin aiki, da kuma yadda ake amfani da ingantattun dabarun noma da sabbin fasahohi a kan amfanin gonakin da IAR ke da hurumi a kansu, wato: masara, dawa, wake, gyada, auduga, artemisia, da castor.

Mahalarta sun hada da masana kimiyya, ma’aikata masu fasaha, jami’an yada ilimin noma, dalibai da manoma, inda suka yi musayar ra’ayoyi da tattaunawa tare da neman hanyoyin hadin gwiwa.

Hakan ya tabbatar da cewa akwai dankon zumunci tsakanin binciken kimiyya da aikin noma na hakika, wanda hakan ke kara inganta amfanin bincike ga al’umma.

Taron Farm Walk na shekarar 2025 ya kara tabbatar da matsayin IAR a matsayin cibiyar binciken noma ta farko a Yammacin Afirka, tare da karfafa dangantaka tsakanin jami’a da al’ummar manoma.

Ranar ta kasance ranar  koyo da sada zumunta da samun haɗin gwiwa wajen bunkasa harkar noma da bincike a Najeriya.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments