Wanene Dakta Muhammad Sani Uwaisu Garkuwan Kudun Zazzau?
Daga Idris Umar Zariya
Dakta masu karatu za su so su ji sunanka daga bakinka mai albarka?
Dakta Uwaisu:
Toh, Bismillahirrahmanirrahim. Da farko, sunana Dakta Muhammad Sani Uwaisu, Certified National Accountant, kuma ni ne Garkuwan Kudun Zazzau.
To Dakta za mu so mu ji takaitaccen tarihin rayuwarka?
Dakta Uwaisu:
Toh, daga farko dai, an haifeni a garin Shika cikin karamar hukumar Giwa a ranar 17 ga watan Yuli, shekarar 1967. Na yi makarantar firamare a nan Shika daga 1973/74 zuwa 1979/80.
Daga nan na tafi sakandare a GSS Musawa a 1980, daga bisani na dawo makarantar gaba da firamare ta Giwa inda na kammala a 1985.
A 1986 na tafi Kaduna Polytechnic, na karanci Diploma a fannin saye da sayarwa (Purchasing and Supply), na kammala a 1989. Sai na kara komawa na yi HND a fannin daya daga 1989 zuwa 1990.
A tsakanin 1989 da 1992, na yi aiki a kamfanin Lema Jibril a Udawa da kuma Project West Africa da ke bayan Ideal Flour Mills Kaduna.
A 1992 na fara bautar kasa a FCE Zaria (wadda yanzu aka maida Federal University of Education Zaria), inda na cigaba da aiki tun daga 10 ga Nuwamba, 1993.
Na fara a matsayin Store Officer, daga baya na koma Purchasing and Supply, daga bisani na koma layin Accounting. A ranar 1 ga Oktoba na zama babban ma’aji na makarantar har zuwa 27 ga Satumba, 2024. Yanzu haka ina hutun Sabbatical a Federal Polytechnic, Bichi.
Toh Dakta, wasu abubuwa ne suka fi burgeka a rayuwa da aiki?
Dakta Uwaisu:
Na yi gwagwarmaya a fannin kare hakkin ma’aikata. Na zama shugaban kungiyar ma’aikata a FCE Zaria, daga baya na zama Sector President, sannan National President.
Na kafa sabuwar kungiya ta SUCUN — Senior Staff Union in Colleges of Education Nigeria. Ni ne na assasa ta, na rajista da ita kuma ni ne shugabanta na farko.
Har ila yau, bayan na zama Bursar, aka nemi in jagoranci kungiyar Bursars na irin wadannan makarantun gaba da sakandire a fadin kasa.
Amma daga baya na ajiye wannan domin samun natsuwa da niyyar kara taimakon al’umma.
Dakta, da alama kana da burin ci gaba da hidima ga jama’a. Menene burinka a halin yanzu?
Dakta Uwaisu:
Eh, gaskiya jama’a da dama suna kiran mu don mu tsaya mu wakilce su, musamman saboda irin rawar da muka taka a baya.
Muna sha’awar kawo ci gaba, musamman ga matasa. Halin da matasa ke ciki yana daga cikin abubuwan da ke damuna. Rashin aikin yi, karancin ilimi da kuma matsalolin tsaro na daga cikin kalubalen da ke bukatar kulawa.
Saboda haka, burina shine in samu dama ta siyasa ko wakilci domin kawo sauyi. A taimaki matasa, a bunkasa noma da sana’o’in dogaro da kai, a tabbatar da tsaro da ilimi.
Wani sako kake da shi ga shugabanni da al’ummar ka?
Dakta Uwaisu:
Ina kira ga sarakuna, limamai, da shugabannin gargajiya da su hada kai da mu. Mu taimaka wa matasa, mu koya musu harkar neman arziki da ilimi, mu tseratar da su daga fadawa tarkon miyagun halaye.
Duk inda na je, zuciyata tana tare da Shika. Ni dan kauye ne, kuma har gobe ina zaune a garin Shika. Ina alfahari da hakan.
Mun gode sosai da wannan bayani Dakta.
Dakta Uwaisu:
Ni ma nagode. Allah ya taimaka ya sa mu ci gaba da hidima da gaskiya da rikon amana. Wassalam.
0 Comments