Mai martaba sarkin Zazzau ya sauke Dagaci bisa laifin bayar da Sarautar Sardauna a garin Samaru
Daga Zakiyya Hamisu Zariya
Mai martaba sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli ya sauke wani Dagaci a gundumar Basawa ƙaramar hukumar Sabon Gari Zariya jihar Kaduna.
Kamar yadda kakakin majalisar masarautar Zazzau Malam Kwarbai ya shaida a wata takarda da ya sanya wa hannu a ranar 14/10/2025.
Takardar ta tabbatar da sauke Dagacin Hayin Dogo Samaru Malam Shehu Musa daga kan matsayin sa na Dagaci bisa laifin da majalisar masarautar ta fitar na yin naÉ—i bada sanin ta ba
Majalisar masarautar ta Zargin Dagaci mai suna malam Shehu Musa da laifin bayar da sarautar Sardaunan Hayin Dogo ba tare da sanin majalisar masarautar ta Zazzau ba.
Sanarwan taci gaba da cewa Dagacin ya yi daɗin wani mai suna Usman Baba Abubakar ba tare da sanin hakimin saba kuma a daidai lokacin da mai martaba sarkin na Zazzau ya ke karrama tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Manadi Sambo da muƙamin Sardaunan Zazzau wanda hakan ke nuna rashin ɗa'a ga masarautar ta Zazzau.
Bisa wannan dalili ne majalisar masarautar ta Zazzau bisa umurnin Sarkin na Zazzau aka dakatar da Dagacin daga kan muƙamin sa da wanda ya naɗa a matsayin Sardaunan Hayin Dogon.
A karshe sanarwan ta ja hankalin wanda Dakacin ya naɗa da cewa kar ya kuskura ya ƙara danganta kansa da wannan sarauta domin Masarautar Zazzau bata san dashiba.
A karshe sanarwan ta gargadi dukkan Hakimai da sarakuna da su guji yin naÉ—i ba tare da sanin majalisar masarautar ta Zazzau ba tace duk wanda yayi majalisar zata daukar masa mataki mai zafi .
Jaridar HAUSA MEDIA REPORTERS ta nemi jin ta bakin Dagacin da aka sauke don jin ta bakinsa amma sai yace " Ni bansan komi akan saukeniba amma na gani a (socal Media) amma banga takarda daga mai martaba Sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli ba bisa haka bazance komiba.
0 Comments