Header Ads Widget

Responsive Advertisement

BABBAR MAGANA: Gidan Jarida Ta Maka Kwamishinonin ‘Yan Sanda Na Katsina Da Kaduna Ƙara Kan Kama Ma'aikataci Ba Bisa Ka’ida Ba


BABBAR MAGANA: Gidan Jarida Ta Maka Kwamishinonin ‘Yan Sanda Na Katsina Da Kaduna Ƙara Kan Kama Ma'aikataci Ba Bisa Ka’ida Ba

A yau gidan jaridar Leadership Hausa Online ta shigar da ƙorafi a gaban Hedkwatar ƴan sanda ta ƙasa, a sashen da ke kula da ƙorafe-ƙorafen jama’a wato Complaint Response Unit (CRU), kan kama ɗaya daga cikin ‘yan jaridunta, Zuhair Ali Ibraheem II, ba bisa ka’ida ba tare da ƙwace masa kayan aikinsa.

A cewar gidan jaridar, waɗanda ake ƙorafin sun haɗa da Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina da na Jihar Kaduna, bisa zargin cewa jami’ansu sun kama ɗan jaridar ne ba tare da wani dalili na doka ba.

Gidan jaridar ta bayyana cewa kayan aikin da aka kwace daga hannun ɗan jaridar sun haɗa da kyamarar Canon, laptop, microphone mara waya, memory card, da kuma kuɗi Naira dubu 65.

A cewar ƙungiyar, jimillar kuɗin kayan da aka kwace aƙalla zasu iya kaiwa akalla Naira miliyan (₦22,000,000) zuwa sama.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ana jiran a saka ranar zaman sauraron ƙarar tsakanin ƙungiyar da jami’an ƴan sanda da kuma wanda

Post a Comment

0 Comments