Header Ads Widget

Responsive Advertisement

CIKAR MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU SHEKARU BIYAR BISA KARAGAR MULKIN MASARAUTAR ZAZZAURa


CIKAR MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU SHEKARU BIYAR BISA KARAGAR MULKIN MASARAUTAR ZAZZAU

Daga Zakiyya Hamisu Zariya

A jiya Shugabar Majalisar Gudanarwa na Jami'ar Jos, Sanata Grace Bent, CON, ta jagoranci tawaga na membobin Majalisar Gudanarwan Jami'ar wajen gabatar da ziyaran taya murna ga Uban Jami'ar,  Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR bisa cikansa Shekaru Biyar a kan Karagar Mulkin Masarautan Zazzau. 
A lokacin gabatar da wannan ziyara, Sanata Grace ta gabatar da bayanai bisa ayyuka da abubuwan da ke wanzuwa a cikin Jamai'ar ga Uban Jami'an. Ta kara da gabatar da godiyansu bisa kan ci gaban da wannan Jami'a take samu bisa Kyawawan shugabancin Mai Martaba Sarkin Zazzau.

Post a Comment

0 Comments