Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari Yayi Maraba da Shigowar Hon. Sadiq Ango APC
Daga Idris Umar, Zariya
Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria, yayi maraba da Hon. Sadiq Ango Abdullahi cikin girmamawa da farin ciki, bisa shigowarsa jam’iyyar All Progressives Congress - APC.
Hon. Albani ya bayyana wannan sauyin sheka da Hon. Sadiq yayi a matsayin babban cigaba na siyasa, wanda ke nuna amincewa da jagorancin jam’iyyar APC a matakin kasa da na jiha, karkashin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Senator Uba Sani na Jihar Kaduna.
Shugaban ya jaddada cewa, Hon. Sadiq na da kwarewa da kuzari da hangen nesa, wanda hakan zai kara karfi da kuzari ga jam’iyyar APC musamman a yankin Sabon Gari da Zariya baki daya.
“Muna maraba da Hon. Sadiq cikin iyalin jam’iyyar APC. Wannan mataki daya dauka alama ce ta kishin cigaba da hadin kai. Muna fatan yin aiki tare da shi domin cigaban karamar hukumar mu da jihar baki daya,” inji Hon. Albani.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar masa da cikakken goyon baya da hadin kai wajen sauke nauyin sa cikin jam’iyyar da kuma gina ingantacciyar makoma ga al’umma Sabon Gari.
0 Comments