Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Mutum kusan 20 tare da Dabbobi ne suka mutu A Haɗarin Tirela


YANZU-YANZU: Mutum Sama Da 20, Tare Da Dabbobi Da Dama Sun Mutu A Haɗarin Tirela

Da safiyar Litinin ɗin nan ne aka samu wani mummunan haɗarin motar dakon kaya ta tirela, wanda ganau suka ce adadin waɗanda suka mutu a nan take sun fi mutam 20, yayin da wasu da dama da suka jikkata, inda aka garzaya da su zuwa cibiyoyin kula da lafiya mafi kusa. Haka kuma an yi asarar dabbobi da dama.

Labaran da muka samu ya nuna cewa tirelar tana kanyar ta ne daga garin Lapai Zuwa Suleja dukkan su a jihar Neja.

Waɗanda wannan abu ya faru a gaban su, sun bayyana cewa motar ta ƙwace wa Direban ne a daidai wata gajeruwar Kwana, wanda hakan ya haifar da birkicewar ta har wannan mummunan haɗari ya faru.

Tuni dai Jam'ian Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), tare da haɗin gwiwa da 'yan sa-kai da sauran al'umma suka hallara a wajen don kai ɗauki.
 
Hukumomi da sauran jama'a masu nazarin al'amuran yau da kullum sun jima suna jan hankali game da haɗari da rashin dacewar loda kaya, ko dabbobi, tare da mutane, wanda an jima ana samun asarar rayuka da dukiya a irin wannan yanayi.

A nan, jaridar HAUSA MEDIA REPORTERS na yin kira ga Hukukomin kiyaye haɗurra, jami'an ' yan sanda, su haɗa kai kai ƙungiyoyin sufuri don kawo ƙarshen wannan abu, tare da ɗaukar mataki mai gauni ga duk wanda ya yi kunnen ƙashi.

Yanzu haka ana ta kokarin sanar da dagi da makusantar wanda suka rasu halin da ake ciki.

Post a Comment

0 Comments