Labari mara daɗinji Ƴan Bindiga Sun Kashe Shugaban Makaranta a Karfi, Jihar Katsina
Wasu gungun ƴan bindiga sun kai hari a daren jiya a garin Karfi da ke cikin ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda suka kashe shugaban makarantar firamare ta Mararrabar Ƙankara, Malam Shamsuddeen Ishaq Karfi.
Majiyar yanar gizo ta Funtua Post ta tabbatar da faruwar lamarin ta wajen iyalan Marigayin da kuma mazauna yankin da lamarin ya shafa. Marigayin ya rasu ne sakamakon harbin bindiga da ƴan bindigar suka yi masa yayin harin da suka kai a cikin dare.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da jana’izarsa tare da wasu da suka mutu a harin. Wannan hari ya zo ne bayan kashe wani Alhaji Gambo a cikin daren jiya a wannan yanki, lamarin da ke ƙara fargaba da damuwa a tsakanin al’ummar Malumfashi.
Yanzun haka hukumomi na biyar lamarin tare da daukar kwarara matakai dai dai gwargwado.
0 Comments