An Sami Kyakkyawar Dangantaka Tsakanin Jami’ar ABU da Karamar Hukumar Toro
Daga Idris Umar, Zariya
A wani yunkuri na haɓaka harkar ilimi da ci gaban al'umma, shugaban Karamar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, Hon. Abubakar Ibrahim Dambo, ya kai ziyarar aiki ga mukaddashin shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, Farfesa Ahmad Adamu.
Farfesa Ahmad ya nuna farin cikinsa da wannan ziyara, inda ya tabbatar da niyyar jami’ar na haɗa kai da Karamar Hukumar Toro wajen bunƙasa ilimi da wasu sassa na ci gaban rayuwa. Ya yaba da kishin ilimi da shugabannin karamar hukumar ke da shi.
Hon. Abubakar Ibrahim Dambo ya godewa jami’ar bisa kyakkyawar tarba, yana mai cewa Toro za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ABU domin buɗe damammaki ga matasa, musamman a fannin ilimi.
Tawagar ta kuma kai ziyara Cibiyar Karatu daga Nesa (Distance Learning Center) ta jami’ar, inda suka tattauna da shugaban cibiyar, Farfesa Muhammad Bashir Mu’azu. An cimma matsaya kan yadda za a ba matasan karamar hukumar damar yin karatu daga nesa cikin sauƙi da inganci.
Hon. Abubakar ya bayyana cewa wannan ziyara za ta buɗe sabon babi na ci gaba da ilimi a Toro da Jihar Bauchi baki ɗaya, tare da godewa dukkanin shugabannin da suka tallafa musu, ciki har da kansaloli da shugabannin shiyya.
0 Comments