GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA AZA HARSASHIN GININ SABUWAR TASHAR MOTOCI DA ZATA YI DAIDAI DA ZAMANI
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani, ta aza harsashin ginin sabuwar tashar Motoci ta zamani a Sobawa dake karamar hukumar Igabi ta Jihar, wani babban aikin samar da ababen more rayuwa da nufin inganta tsaro ga fasinjoji da inganta tsaftar muhalli, da bunkasa tattalin arziki a Jihar.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan ya yi kira ga mazauna yankin da masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken goyon baya don ganin an kammala aikin a kan lokaci, tare da bayyana muhimman dabarunsa wajen inganta harkokin sufuri na cikin gida da kuma bunkasa matsayin Jihar Kaduna matsayin cibiya a bangaren shige da ficen Jihohi a fadin kasarnan.
Ya jaddada cewar aikin ginin tashar da Kamfanin gine-gine na Sky Habitat Construction & Real Estate zata yi zaa kammala shi nan da watanni 8 masu zuwa.
Gwamnatin Jihar na fata kakkabe dukkan wasu tashoshi da basa karkashin hukumomi saboda batun tsaro.
A lokacin gabatarwa akwai jagororin kungiyar direbobi ta kasa NURTW reshen Jihar Kaduna karkashin jagoranci Alhaji Aliyu Tanimu Zaria, ya jaddada godiya ta musamman ga Sanata Uba Sani, cewar sa salon daya dauka na magance matsalolin tsaro Direbobi ayyukan su na Sufuri ya inganta sun dena kwana da yinwa.
0 Comments