Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Karamar Hukumar Sabon Gari Ta Kare Sheikh Jamilu Albani Daga Zargin Da Ake Masa


Karamar Hukumar Sabon Gari Ta Kare Sheikh Jamilu Albani Daga Zargin Da Ake masa

Daga Abubakar Musa,Zariya

Ofishin Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari ya musanta zarge-zargen da aka yi wa Sheikh Jamilu Abubakar Albani, wanda shi ne Kwamaredin Kwamitin Tsayuwar Daga Na Gasa Karatun Al-Qur’ani (KSCQRC) a Jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, karamar hukumar ta bayyana takardar korafin da aka aika wa Gwamna Uba Sani a matsayin "mugunta ce, siyasa ce kawai, kuma ba ta da tushe."

Sanarwar ta jaddada sadaukarwar Sheikh Albani wajen bunkasa ilimin Qur’ani a jihar Kaduna tsawon fiye da shekaru goma, tana nuna irin yadda yake amfani da dukiyarsa wajen ganin nasarar gasar karatun Al-Qur’ani tun daga shekarar 2015.

Game da zargin amfani da motar Sienna ta gwamnati ba bisa ka’ida ba, karamar hukumar ta bayyana cewa motar tana hannun kwamitin ne, kuma ana amfani da ita ne kawai don ayyukan hukuma. An cire alamar gwamnati a jikin motar ne saboda dalilan tsaro, don kauce wa satar mota da kuma amfani da ita ba da izini ba.

Dangane da shiga Sheikh Albani cikin harkokin siyasa, sanarwar ta kare shi da cewa wannan matsayi nasa ya taimaka wajen samo karin tallafi da albarkatu domin ci gaban ilimin addinin Musulunci.

Sanarwar ta kara da cewa wadanda suka rubuta korafin suna da bukatu na kashin kansu, ba wai damuwar al’umma ba ce.

“Muna nan daram tare da Sheikh Jamilu Albani. Muna da cikakken imani da gaskiyarsa da jagorancinsa,” in ji sanarwar, tana mai kira ga gwamnati da al’umma da su yi watsi da wannan “kagaggen zargi da ke neman raba kan jama’a.”

Karamar Hukumar Sabon Gari ta kuma sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Uba Sani tare da kira ga jama’a da su mayar da hankali wajen hada kai da ci gaba da tallafawa ilimin Qur’ani a jihar.

Post a Comment

0 Comments