Majalisar Matasa (NYCN)Ta Yi Watsi da Zarge-Zarge Akan Sheikh Jamil Albani Samaru
Daga Abubakar Musa Kaduna
Majalisar Matasan Ƙasa reshen ƙaramar hukumar Sabon Gari ta yi watsi da zarge-zargen da wasu ke yaɗawa kan fitaccen malamin addini, Sheikh Abubakar Jamil Albani na Samaru. Majalisar ta bayyana cewa ba su ga wata alamar gaskiya ko shaidar da ke nuna sahihancin zarge-zargen ba, sai dai son zuciya, hassada, da kokarin tayar da fitina a cikin al’umma.
A wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a Zariya, shugaban majalisar matasan, Kwamared Jibril Salishi, ya bayyana cewa nazari da binciken da suka gudanar ya nuna cewa koken da ake yadawa ba shi da tushe, kuma ya na ɗauke da alamomin siyasa da kullin batar da suna.
> “Koken nan ya zo ne a lokacin da Sheikh ke ƙara samun karbuwa da girmamawa daga al’umma. Tambayar ita ce: ina kuka kasance shekaru da suka wuce?” in ji Salishi.
Shugaban ya ce koke ɗin na ɗauke da sunaye da sahannun wasu da ba su san da lamarin ba. Ya kara da cewa, idan har zarge-zargen gaskiya ne, me ya kawo siyasa cikin lamari da ya shafi addini?
Majalisar ta bayyana cewa Sheikh Jamil Albani ya shafe fiye da shekaru goma yana hidima ga al’umma da wayar da kai kan addini cikin gaskiya da tawali’u. Har ila yau, matasan sun kafa wani kwamiti na musamman don zurfafa bincike kan lamarin, tare da shaida cewa za su dauki matakin da ya dace akan duk wanda aka tabbatar yana yada ƙarya.
Kwamared Salishi ya roki malamai da shugabannin addini da su kauce wa kiyayya da son zuciya, yana mai kira da a yi amfani da addini wajen haɗa kan al’umma, ba raba su ba.
A ƙarshe, Majalisar Matasan ta nuna cikakken goyon bayanta ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Malam Uba Sani, da shugaban karamar hukumar Sabon Gari bisa jajircewarsu wajen warware matsalolin da suka shafi zaman lafiya da ci gaban al’umma.
> “Muna rokon Allah ya zaunar da jiharmu da ƙasarmu baki ɗaya cikin zaman lafiya da fahimta,” in ji shugaban majalisar a karshe
0 Comments