Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta gayyaci Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, domin bayyana a gaban Sashen Bincike na Musamman na ‘Yan Sanda (FID) kan wani lamari da aka ce ya faru a lokacin bukukuwan Sallah a masarautarsa.
Wata takardar gayyata da aka rubuta a ranar 2 ga Afrilu, 2025, wadda Kwamishinan ‘Yan Sanda (OFS), CP Olajide Rufus Ibitoye, ya sanya wa hannu a madadin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Bincike (FID), ta bayyana cewa an umarce su da gayyatar Sarkin domin gudanar da wani muhimmin bincike.
Takardar ta bayyana cewa an bukaci Sarkin da ya halarci wajen binciken da za a gudanar a ofishin FID da ke gabanin hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Area 11, Abuja, da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025.
Takardar ta kara da cewa ana bukatar halartar Sarkin ne domin bayar da gudunmawa a wani bincike mai muhimmanci.
0 Comments