Header Ads Widget

Responsive Advertisement

SSANU da NASU reshen ABU Zariya sun tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar manyan ma'aikata da ƙanana reshen ABU sun tsunduma yajin aikin a yau Litinin

Daga  Umar I Samaru 

Ƙungiyoyin ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello Zariya sun tsunduma yajin aikin sai Baba ya gani sakamakon rashin biyan su albashi wata huɗu da gwamnati tayi

Gamayyar ƙungiyoyin (JAC), waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASU) da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i na Najeriya (SSANU).

A cikin wata sanarwa da uwar kungiyar  ta aike wa dukkanin shugabannin ƙungiyar da ke jami’o’i da su fara yajin aikin a ranar Lahadi.

Sanarwar, wadda Sakataren NASU, Mista Peters Adeyemi da Shugaban SSANU, Mista Mohammed Ibrahim, suka sanya wa hannu, a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce: “Mun yanke wannan hukunci ne sakamakon dakatar da albashinmu na wata huɗu.”

Duk da cewar Shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan kashi 50 na albashin da aka dakatar, amma JAC ta ce babu wanda ya samu ko sisi daka cikinsu.

JAC, ta bayyana cewa ta gargaɗi gwamnati a lokuta daban-daban, amma ba a yi komai kan buƙatarsu ba.

Saboda haka, JAC ta yanke shawarar cewa za a fara yajin aikin ne misalin ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024.

Ƙungiyar ta ce sai gwamnati ta waiwaye su sannan za su janye yajin aikin da za suka fara a daren Lahadi.

Bisa wannan umurni ne tuni Kwamret Muhammad A Yunusa ya tara dukkan ya'yan kungiyar ta ƙasa reshen ABU Zariya don bin umurnin uwar kungiyarsu ta ƙasa tare da basu dokar tsunduma cikin yajin aikin kai tsaye.

Wakilinmu ya zagaya cikin harabar jami'ar don ganin tasirin yajin aikin da suka fara 

Tabbas yanzu haka dukkan ofis-ofis an fara garƙamesu da kwaɗo a dukkan harabar ta jami'ar kuma ma'aikata duk sun koma gidajensu don yin biyayya ga uwar-Kungiyar tasu.

Post a Comment

0 Comments