Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Rundunar ƴan Sanda ta kama mai garkuwa da mutane, tare da ƙwato kuɗin Fansa

Rundunar ƴan Sanda ta kama mai garkuwa da mutane, tare da ƙwato kuɗin Fansa

Rundunar ƴan Sandan Jihar Nasarawa ta cafke wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da kwato kuɗin Fansar da suka karɓa har Naira dubu dari biyar da arba’in da bakwai (547,000).

Kakakin Rundunar ƴan Sandan Jihar Nasarawa Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

A cewar Nansel, kudaden ana zargin na daga cikin kasonsa na kuɗin fansar da suka karba bayan yin garkuwa da wani Bafulatani Cironman Arugbadu da ke karamar hukumar Eggon ta Jihar Nasarawa.

Kamar yadda Sanarwar ta bayyana, an kama wanda ake zargin a yau 27 ga watan Oktoban 2024 da misalin karfe 11:30 na safe, Rundunar haɗin guiwar Jami'an tsaro na ƙaramar Hukumar Eggon sun kama wani Abdulkarim Zakari da ke kauyen Konba a karamar hukumar Wamba ta Jihar Nasarawa bisa zargin yin garkuwa da mutane.

“Da aka yi masa tambayoyi, ya amsa cewa yana cikin Tawagar da ta yi garkuwa da Ciroman Fulani a Arugbadu inda suka karbi kudin fansa Naira Miliyan 5, kuma an ba shi kasonsa Naira Miliyan daya da dubu dari biyu.

Ya ci gaba da cewa Kwamishinan ƴan Sanda Umar Shehu Nadada ya bayar da umarnin a farauto sauran ƴan Tawagar da suka aikata laifin tare.

Post a Comment

0 Comments