Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Jaridar Yanar Gizo: Aikin Jarida A Yanar Gizo Da Ɗan Soshal Midiya, Tarihi, Asali Da Bambancinsu


Jaridar Yanar Gizo: Aikin Jarida A Yanar Gizo Da Ɗan Soshal Midiya, Tarihi, Asali Da Bambancinsu

Daga Ɗanjuma Katsina

Masana tarihi sun ce aikin jarida ya faro ne daga halittar ɗan'adam wato neman sani, neman ilmi a kan wani abu faɗakarwa da nishaɗantarwa.
aikin jarida bisa tsari na farko an fara shi ne da hawa bisa wani tudu a ba da labari, inda wani mutum kan hau, jama'a su kewaye shi yana ba da labari ko na faruwar wani lamari, ko na nishaɗi, ko na an kararwa a kasuwanni ko wajen taruwar jama'a.

Matakin aikin jarida na biyu shi ne wanda aka fara a takarda, wanda ake ce wa jarida.

Mataki na uku shi ne na rediyo.  Na huɗu kuma shi ne na talabijin.

JARIDA A YANAR GIZO
 
A shekarar 1993, kamfanin The News And Observer Newspaper A Raleigh, a North Carolina ta ƙasar Amurka suka fara samar da labarai a yanar gizo inda suka samar da wani shafi mai suna NANDO TIMES masu ba da labarai a yanar gizo awa 24.

A Nijeriya jaridar farko da ta fara bugawa a takarda kuma a yanar gizo ita ce Post Express da ake bugawa a Legas a shekarar 1996, kamfanin bai daɗe ba ya rufe saboda ba riba.

A shekarar 2003 wani ɗan jarida mai suna Tony Iyare ya ƙaddamar da jaridar The Gleaner News Online, amma shi ma rashin samun kuɗin shiga ya sanya dole ya rufe ta.

Wasu 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje sun fara kafa jaridu a yanar gizo Jonathan Elendu ya kafa elendureports.com a shekarar 2004. Sai Sunny Ofili ya ƙaddamar da timesofnigeria.com a shekarar 2005. 

Omoyele Yele Sowore ya kafa kamfanin Sahara Reporters a shekarar 2006.

A shekarar 2008 Dele Olojede ya kafa 234next.com q nan Nijeriya a Legas. Ita ma bayan shekara biyu ta mutu.

Jaridar farko a yanar gizo da aka fara kafawa mai ƙarfi kuma ta ɗore har yanzu a Nijeriya ita ce PREMIUM TIMES, wadda aka kafa ta a birnin Abuja, wanda Oyedapo Oyekunle Dapo Olorunyomi da Musikilu Mojeed suka kafa.

PREMIUM TIMES ana iya kiran ta babbar jaridar yanar gizo da ba kamar ta a Nijeriya.

KAFUWAR JARIDUN YANAR GIZO A NAJERIYA 

Manyan 'yan jaridun da suka bar aiki suna zaune a gida suka fara kakkafa jaridun yanar gizo a Legas. Wasu tsaffin editoci ne a manyan jaridu da mujallun ƙasar nan.

Wannan ya sanya mafi yawan ingantattun  jaridun yanar gizo suna a Legas da Abuja.

A arewa masu Yamma jaridar yanar giza ta farko da ta fara suna nan da nan ita ce DAILY NIGERIA, wadda ɗan jarida Jafar Jafar ya kafa a ranar 6 Maris, 2016. Labaranta na rikicin sarautar Kano da kuma na bidiyon zargin saka Dala aljifu ne suka fara fito da ita duniya ta san ta.

Ɗaya daga cikin jaridun yanar gizo na farko-farko masu tasiri a yankunansu da kuma Arewa gaba ɗaya, akwai jaridar TASKAR LABARAI da KATSINA CITY NEWS da ta koma KATSINA TIMES wadda ke kan www.katsinatimes.com.da WIKKI TIMES a Bauchi da SOLABASE  da sauransu.

Kafa ƙungiyar 'yan jaridar yanar gizo da ake kira GOCOP a taƙaice aranar 9 Oktoba, 2023 wasu tsaffin 'yan jarida da suka kafa jaridun yanar gizo su 10 ne suka haɗu a Legas don kafa ƙungiyar, waɗanda daga baya suka zaɓi shugabannin wucin-gadi, kamar haka Musikilu Mojeed na PREMIUM TIMES a matsayin shugaba, Dotun Oladipo na The Eagle Online a matsayin Sakatare, sai Maureen Chigbo ta REALNEWS Magazine a matsayin Ma'aji. Daga baya aka zaɓi Ɗanlami Nmodu a matsayin mataimakin Shugaba na shiyyar Arewa.

Daga cikin waɗanda suka taimaka a ƙungiyar akwai Yusufu Ozi Usman na GREENBARGE REPORTERS, wanda yake tsohon ɗan jarida ne.

Ƙungiyar ta samu cikakkiyar rijista bayan shekaru ana faɗi-tashi a ranar 22 ga Oktoba, 20215, kuma aka ƙaddamar da ita Eko Suits Hotel da ke Legas.

Shugabancin  MureenChigbo, wanda ya fara a 2021 ya haɓaka ƙungiyar ta fara gogayya da tsaffin ƙungiyoyin 'yan jarida a ciki da wajen ƙasar nan.

Yanzu ƙungiyar tana da membibo masu jaridun yanar gizo su 120 a ƙasar nan, kuma dukkaninsu mallakar 'yan jaridar da suka fito daga kofofin watsa labarai daban-daban ne.

Daga cikin membobin har da KATSINA TIMES, wadda shugabanta ke ciki kwamitin shirya taron shekara-shekara na ƙungiyar.
 
Daga cikin manufofin ƙungiyar akwai kare martabar aikin jarida a aikin jarida na yanar gizo.
A afrilun 2025 suka kaddamar da wani littafin da ya kumshi tarihin kafuwar kungiyar da kundin tsarin mulkinta da kuma hotuna da jaridun membobin ta da tarihin aikin jarida a duniya da kuma Najeriya. Littafin mai suna Nigeria media renaissance..Gocop perspectives on online publishing. Taron anyi shi a dakin taron Sheraton hotel.an kuma kaddamar da gidauniyar kudin da za a kafa hedkwatar kungiyar a legas. 

Ɗan Soshal Midiya a aikin jarida 
Soshal Midiya wasu kafafen sada zumunta ne da aka ƙirƙira daban a duniya irin su Facebook, Twitter, wanda yanzu ya koma X sai Tiktok, Telegram, Instagram, WhatsApp da sauransu.

Dandali ne da aka kafa don isar da kowane saƙo ba tare da kowace ƙa'ida ba, in ban da wadda su masu kamfanin suka kafa.

Ɗan Soshal Midiya shi ne wanda aikin sa shi ne amfani da wannan kafar don isar da saƙonsa ba tare da la'akari da kowace ƙa'ida ko doka in ban da wadda kamfanin ya kafa don buƙatar kansa ba.

Ɗan Soshal Midiya na iya zama ɗan jarida mai zaman kansa idan ya san ƙa'idar aikin jarida da dokokinsa, kuma yana kare su a duk rahotanni da zai watsa a shafukansa.

Yana iya shiga ƙungiyoyin 'yan jarida in har ya cika sharaɗin da  tsarin mulkin ƙungiyoyin suka kafa.

Misali a kundin tsarin mulkin ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa (NUJ), an bayyana ƙarara cewa kafin ɗan jarida ya zama mamba sai yana da aƙalla babbar diploma (HND) a kan aikin jarida, ko kuma yana aiki a wani gidan jarida na aƙalla shekaru 15.

A kundin tsarin mulkin  'yan jarida da ke yanar gizo (GOCOP), sai ɗan jarida ya kai matsayin Edita a wani gidan jarida kafin ya shige ta.

Idan ɗan Soshal Midiya yana yaɗa kome ba kula da ƙa'ida da dokokin aikin jarida, ya zama cikakken ɗan Soshal Midiya.

Idan ɗan Soshal Midiya yana neman sani da aikata da kare duk ƙa'idar aikin jarida a aikinsa yana iya zama ɗan  jarida.

Zama ɗan ƙungiyar 'yan jarida, kuma sai abin da tsarin mulkin kowace ƙungiya ta ce.

Ɗanjuma Katsina shi ne mawallafin jaridun KATSINA TIMES MEDIA GROUP.

Post a Comment

0 Comments