An Yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gyara Hanyar Kagarko Zuwa Hure
Daga Idris Umar, Kaduna
Shugaban matasan ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na Arewa maso Yamma, Alhaji Aminu Jibirin, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta gaggauta gyara hanyar da ta tashi daga Kagarko zuwa Hure, sakamakon lalacewar da hanyar ke fama da ita tsawon lokaci.
Alhaji Aminu Jibirin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai yankin tare da wasu abokansa a cikin makon da ya gabata, inda suka tabbatar da halin Æ™uncin da al’ummar yankin ke ciki, musamman a lokacin damina.
A cewarsa, "Yakamata gwamnatin jihar Kaduna ta duba wannan hanya da gaggawa domin mutanen yankin sama da dubu 30 ne ke amfani da ita a kullum, kuma suna taka muhimmiyar rawa a fannin siyasa da ci gaban jihar."
Shugaban matasan ya ƙara da cewa rashin hanyar mota mai kyau na jefa mazauna yankin cikin matsaloli, musamman lokacin da ake buƙatar kai marasa lafiya zuwa asibitoci ko kuma a lokacin safarar kayayyaki.
Ya yi roÆ™o ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da sauran masu ruwa da tsaki a matakin jiha da na tarayya da su sa hannu wajen ganin an gyara wannan hanya domin ceto al’ummar yankin daga halin da suke ciki.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa lokacin damina na daga cikin mafi wahala ga mazauna yankin, inda hanyoyin su kan zama marasa amfani, lamarin da ke jefa su cikin tsananin ƙunci.
A ƙarshe, Alhaji Aminu Jibirin ya nuna godiyarsa ga sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin unguwanni da na ƙaramar hukumar Kagarko bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda a faɗin yankin da ma jihar baki ɗaya.
0 Comments