Zaben Cike Gurbi: Na ji dadin yadda ‘yan jam’iyyar APC suka fito, muna fatan lashe zaben, in ji Shatiman Basawa
Daga Abubakar Musa, Kaduna
A yayin da aka soma zaben cike gurbi na dan majalisar jiha na mazabar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna a ranar Asaba, daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a karamar hukumar Sabon Gari ya jinjinawa ‘ya’yan jam’iyyarsu ta APC.
Shatiman Basawa Alhaji Sa'eed A . Dada, abokine ga mai girma shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Hon. Jamilu Albani ya nuna jindadinsa bisa yadda yayan jam’iyyar APC suka fito kwansu da kwarkwatansu wajen kaɗawa jam’iyyarsu kuri’a a zaben cike gurbin da yake gudana. Ta
Shatiman Basawa Alhaji A Dada ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a lokacin da Jamɓiyar APC tayi nasa a Akwatin da yake wakilta a garin Basawa .
A bisa haka ne, ya yi fatan cewa jam’iyyarsu ne za ta yi; “nasara a wannan zabe da ikon Allah”, in ji shi.
“wannan zabe ana gudanar da shi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, ga mutane sun fito sosai suna gudanar da zaben su”, ya tabbatar.
“Fatan mu kuma APC ce za ta yi nasara, ko yanzu aka tsaida kada kuri’a za mu ci zabe”, ya tabbatar.
0 Comments