Kungiyar ‘Yan Kasuwar Sabon Gari Zariya na Kira ga Gwamna Uba Sani akan Gyaran Hanyar Kasuwar
Daga Idris Umar, Zariya
Kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari da ke cikin karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ta yi kira ga Gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, da ya cika alkawarin da ya dauka na gyara babban titin kasuwar Sabon Gari Market.
Wannan kiran ya biyo bayan ziyarar da Gwamnan ya kai karamar hukumar a kwanakin baya, inda ya sha alwashin fara aikin cikin sati biyu. Sai dai har yanzu, ba a fara aikin ba, abin da ya haifar da damuwa da kuma rashin jin dadi daga bangaren ‘yan kasuwa.
Shugaban dattawan kungiyar, Malam Aliyu Musa, ya bayyana cewa suna daga cikin masu samar da mafi yawan kudaden shiga ga jihar, amma har yanzu ba a mayar da hankali ga bukatunsu ba. Ya ce rashin gyaran hanyar yana hana ci gaba da kuma haifar da wahala ga masu kasuwanci da masu siye da sayarwa.
Shima shugaban kungiyar direbobin keke-napep, Malam Muhammad Sani Sa’eed, ya bayyana cewa hanyar na jefa su cikin hadurra da asarar kudade, yana mai kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar mataki.
Kwamared Hasan Sandas, sakataren Majalisar Matasa ta Kasa reshen Sabon Gari, ya gargadi gwamnati da cewa idan har ba a dauki mataki ba, za su fuskanci martani daga matasa da kuma ‘yan kasuwa, ciki har da toshe hanyar da kuma amfani da kuri’unsu a zabe mai zuwa.
A nasa bangaren, Sarkin kasuwar Sabon Gari, Malam Iliya Shuaibu, ya roki abokan kasuwanci da su ci gaba da hakuri, yana mai fatan cewa Gwamna Uba Sani da shugaban karamar hukumar za su duba lamarin da gaggawa don kaucewa matsaloli masu tsanani a gaba.
0 Comments