Dole ne mu yaba wa Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na Jihar Kaduna – Kera
Daga Idris Umar, Zariya
Fitacciyar ‘yar siyasa a tafiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, Hajiya Zulaihat Yunusa (Kera), ta bayyana jin dadinta da gamsuwarta da irin jajircewa da ƙoƙarin da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na jihar, Hon. Sadik Mamman Legos, ke yi wajen kawo ci gaba a jihar, musamman a ɓangaren jin ƙai da taimako ga mata da matasa.
A wata hira da manema labarai a garin Zariya, Kera ta
ce, "Yanzu haka Hon. Sadik Mamman Legos ya zama uba mai kulawa da marayu da talakawa a fadin Jihar Kaduna." Ta ƙara da cewa yana taka rawar gani wajen share wa mata hawayensu ta hanyar samar da hanyoyin dogaro da kai da kuma sauraren koke-koken jama’a ba dare ba rana.
Kera ta jinjina wa yadda Karamar Hukumar Kaduna South ke ci gaba da samun sauyi da bunƙasa, duk bisa ga jajircewar samun mutum irin Legos a matsayin mai wakilci da jagoranci. Ta ce: "Mun gode wa Gwamna Uba Sani da ya amince da naɗa Hon. Sadik Mamman Legos da Hon. Raiyanu Husaini a matsayin amintattu a muhimman wurare."
Ta yabawa ofishin Uba Sani Support Group da cewa yana taka rawa matuƙa wajen tallafa wa al’umma ta fannoni da dama, karkashin jagorancin Hon. Sadik Mamman Legos.
Har ila yau, Kera ta bayyana rawar gani da Hon. Sadik Mamman Legos ya taka a zaɓen cike gurbi da aka gudanar kwanan nan a Gundumar Basawa. Ta ce, “Lokacin da aka fuskanci matsala a zaɓen dan majalisa na Basawa, mun sanar da shi halin da ake ciki. Cikin gaggawa ya saurare mu kuma ya bayar da gudummawa wadda ta kai mu ga nasara cikin salama da zaman lafiya.”
A ƙarshe, Hajiya Kera ta mika godiyarta ga Gwamna Uba Sani da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sadik Mamman Legos, bisa yadda suke bai wa mata dama a fannoni daban-daban na siyasa da shugabanci a jihar. Ta yi addu’ar fatan alheri da ci gaba a gare su baki ɗaya.
0 Comments