Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Bikin cikar kungiyar Fumwan shekaru 40 ya samu karɓuwa a Kaduna


Bikin cikar kungiyar Fumwan shekaru 40 ya samu karɓuwa a Kaduna 

Daga Abubakar Musa, Zariya 

Taron an gudanar dashe ne a babban Dakin Taro na Umaru Musa 'Yar'Adua wanda ke Dandalin Murtala Mohamed na Garin Kaduna, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Muslim, Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na Ill, CFR, mni, a Babba Taro na Kasa tare da Bikin Cikar Haddadiyar Tarayyan Kungiyoyin Mata Musulmi Na Nieriya (FOMWAN), shekaru Arba'in da kafuwa.
Wannan taro ya sami halarcin Dokta Suwaiba Sa'eed Ahmed Ministan Ƙasa a Ma'aikatan Ilimi wanda ta wakilci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, sai Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna wanda ta wakilci Gwamna Sanata Uba Sani, sai kuma Farfesa Abduljalal Danbaba wanda ya wakilci Shugaban Majlisar Tarayya Rt. Honarabul Dokta Abbas Tajuddeen, GCON,  Iyan Zazzau.
Har ila yau, Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Lagos Alhaji Lateefa Modupe Okunnu, OFR da Wakiliyar Mai Dakin Shugaban Kasa wanda Hajiya Fatima Abbbas Tajuddeen ta wakilta duk sun kasance a wurin wannan taro.
Hakazalika, Babban Limamin Masallacin Sultan Bello na Kaduna Dokta Muhammad Suleiman da Sheikh Ahmed Abubakar Mahmoud Gumi da Farfesa Salihu Shehu na Jami'ar Bayero duk sun kasance daga cikin al'umomin da suka halarci wannan taro na yàu.
Taron mai taken tallafa ma Mata domin jure chanje-Chanjen yanayi ya sami halarcin baki daga kasashen Amirka da Biritaniya da kasashen makwabtanmu na Nahiyar Afirka.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments