AN KADDAMAR DA MASALLACIN JUMMA'A NA DOKTA YAHYA HAMZA
DA ranan yau, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya kaddamar da Masallacin Jumma'a da Cibiyan Karrattukan Addinin Musulunci na Dokta Yahya Hamza a Garin Rigacikun na Gundumar Rigacikun, Karamar Hukumar Igabi.
Zuri'an Marigayi Dokta Yahya Hamza suka hassasa wannan Masallaci a matsayin sadakatul Jariyya.
Shugaban kwamitin Masallacin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci gabatar da Sallan Jumma'a bayan gabatar da Khuduba inda ya jawo hankalin al'umma bisa muhimmancin Masallaci a rayuwan al'umma.
0 Comments