Wata kungiya mai suna Arewa Progressive Youth karkashin jagorancin Hajiya Ummussalma Isyaka Rabi’u ta gudanar da taron karawa juna sani a Kano, domin nazarin matakan tattalin arziki da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ke aiwatarwa.
Taron ya jawo mahalarta daga jihohi daban-daban na Arewacin Najeriya, inda aka tattauna hanyoyin tallafa wa matasa da rawar da su ke takawa a tsarin tattalin arzikin ƙasa.
Bayan kammala taron, ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, tare da kiran da ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a shekara ta 2027.
Ƙungiyar ta bayyana cewa matakin na da muhimmanci domin tabbatar da dorewar sauye-sauyen tattalin arziki da tsarin mulkin da gwamnatin ke yi.
0 Comments