A yau litinin ne wanda yai dai-dai da 21-07-2025 Senator Babangida Hussaini Walin Kazaure Sanata mai wakiltar shiyyar jigawa arewa maso yamma, ya gudanar da bikin bada tallafin takin zamani ga manoman dake yankin da yake wakilta, an gudanar da wannan biki ne a karamar hukumar Suletankarkar.
Inda ko wacce karamar hukuma zata rabauta da takin tirela guda mai dauke da taki buhu dari shida(600).
Taron ya samu halarta manya-manyan baki da shugabanin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC.
A cikin jawabin sanatan yayi kira ga wakilan da wannan kayan zasu je hannun su da suji tsoran wajen raba wannan kayan domin tabbatar da kayan ya isa inda ake so yaje.
0 Comments