Mai Girma Malam Umar Namadi, Gwamnan Jihar Jigawa, ya halarci Taron Kasuwanci na Najeriya da kasar Masar wanda aka gudanar a hotal din Transcorp Hilton, Abuja.
A wajen taron, Gwamna Namadi ya gayyaci masu zuba jari daga Masar da su ziyarci jihar Jigawa domin gani da idon su dimbin damar zuba jari da ke akwai a jihar, tare da haskaka manufofin jihar na saukaka harkokin kasuwanci, ci gaban ababen more rayuwa da kuma albarkatun noma.
Halartar gwamnan a wannan taro na nuna jajircewar Jihar Jigawa wajen karfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar al’umma.
0 Comments