Rahotanni daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar Kano sun bayyana cewa jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suka fito, sun kama wani matashi mai suna Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello.
Bayanan sun nuna cewa an cafke shi ne da A yau, yayin da yake filin jirgin, sai dai har yanzu ba a bayyana dalilin kama shi ba.
Ana sa ran karin bayani daga hukumomin tsaro a nan gaba domin fayyace musabbabin cafke matashin.
kana Son Kasancewa Cikin Sahun Farko Dake Samun Ingantattun Labarai Shigo Jaridar HAUSA MEDIA REPORTERS a kowani kokaci
0 Comments