Nasarrorin Makarantar Staff school Sun Nuna Cikakken Kudurin ABU Kan Ingancin Ilimi
Daga Idris Umar,Zariya
Daraktan Gudanarwa na Cibiyar Binciken Kiwon Dabbobi ta Ƙasa (NAPRI), Farfesa Mohammed Rabiu Hassan, ya yabawa gagarumar nasarar da Makarantar Ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Staff School) ta cimma, yana mai cewa hakan na nuna yadda jami’ar ke da kwazo wajen tabbatar da ingantaccen ilimi.
Yayin da yake jawabi a matsayin Shugaban Biki a wajen bikin yabo da karramawa karo na 35 na makarantar, Farfesa Hassan ya bayyana cewa makarantar ta kafa wani tushe na kwarewa da zai ci gaba da zama abin koyi.
> “Shigar da Makarantar Ma’aikatan NAPRI cikin tsarin Makarantar Ma’aikata ta ABU da kuma karuwar É—alibai daga 220 zuwa 440 a cikin zangon karatu guda na nuna cewa muna Æ™ara faÉ—aÉ—a damar samun ilimi mai nagarta,” in ji shi.
Farfesa Hassan, wanda ya samu wakilcin Dr. Y. M. Ishiaku, Mataimakin Darakta mai kula da Yada Ilimi da Haɗin Gwiwa na NAPRI, ya jaddada cewa ilimi bai tsaya ga karatun littattafai ba, dole ne a mai da hankali kan koyar da basira da ƙirƙira domin tafiya da zamani.
Ya kara da cewa rawar da iyaye da masu kula da yara ke takawa a ilimantarwa ba ta da wani madadi, inda ya ce halayen da ake dasawa yara daga gida kamar girmamawa, nauyi, da juriya, sune ginshikin É—abi’ar su.
Farfesa Hassan ya godewa shugabannin makarantar bisa gagarumar Æ™oÆ™arin da suke yi, yana mai Æ™arfafa su da su ci gaba da kasancewa fitilu na ilimi da gina É—abi’a. Ya kuma tunatar da É—aliban cewa wannan rana ba Æ™arshe ba ce, illa mataki ne a tafiyar dogon rayuwar karatu da haÉ“aka kai.
Muhimmancin Koyar da Kimiyyar Noma a Makarantar Firamare
A nasa jawabin, bako na musamman, Farfesa Aminu Ahmed Muhammad, Shugaban Sashen Kimiyyar Gona (Agronomy) na Jami’ar Ahmadu Bello, ya gabatar da takarda mai taken: “Muhimmanci da Tasirin Koyar da Kimiyyar Noma a Makarantar Firamare.”
Farfesa Muhammad ya bayyana cewa koyar da kimiyyar noma tun daga makarantar firamare hanya ce ta tabbatar da makoma mai kyau ga yara, inda ya ce hakan na da matuƙar muhimmanci, gaggawa kuma wajibi ne.
> “Wannan darasi yana da nasaba da Æ™alubalen da muke fuskanta yanzu kuma yana da matuÆ™ar muhimmanci ga makomar da muke fatan cimmawa,” inji shi.
Ya kuma bukaci a tsara manhajar karatu ta yadda za a bai wa noma muhimmanci a cikin aji, tare da ƙarfafa gina lambunan makaranta da koyar da noma ta hanyar yara su shiga kai tsaye.
Magatakarda na Jami’ar Ahmadu Bello, Malam Rabiu Samaila, ya samu wakilcin Malam Ishaq Murtala, Mataimakin Magatakarda mai kula da Ci gaban Ma’aikata (HRD).
0 Comments