Header Ads Widget

Responsive Advertisement

jawabin sabon muƙaddashin Shugaban jam'ar ABU a zaman majalisarsa na farko.


Daga Idris Umar,Zariya

Farfesa Adamu Ahmed, wanda ya karɓi ragamar shugabancin Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a matsayin Shugaban Jami’a na 14 a ranar 30 ga Afrilu, 2025, ya bayyana sabuwar manufa mai ƙwarin guiwa domin makomar jami’ar.

A jawabinsa na farko mai cike da ƙarfafawa guiwa da ya gabatar ga Majalisar Jami’ar jiya, sabon shugaban jami’ar ya jaddada cewa salon jagorancinsa zai ta’allaka ne a kan shawara da haɗin gwuiwa da kuma ɗaukar nauyi da karfafa juna.

"Zan fi saurara fiye da magana, kuma zan ɗauki mataki a duk lokacin da ake bukatar hakan," in ji shi, yana kafa harsashin sabon zamani na shugabanci mai buɗaɗɗen ido da jin ra’ayi.

Farfesa Ahmed ya nuna kudirinsa na gina muhalli inda 'yancin fahimta ke bunƙasa, cancanta ke samun karɓuwa kuma gaskiya da bayyananniyar hanya ba zabin ra’ayi ba ne sai dai wajibi.

Ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa ƙirƙira, da 'yancin tunani.

Shugaban jami’ar ya gargaɗi cewa ba za a lamunci kasawaba ko halayyar rashin ƙwarewa ko rashin da’a ba a ƙarƙashin wannan sabuwar shugabanci.

Da wannan tsayayyen matsayi, Farfesa Ahmed ya nuna cewa lokacine na nuna ƙwarewa a Jami’ar ba yin barciba.

Ya bukaci ma’aikata gaba ɗaya su dinga sarrafa zuciyarsu da ra’ayoyinsu, su kuma warware duk wata matsala a cikin tsarin jami’ar, yana jaddada cewa kowanne ma’aikaci – mai koyarwa ko wanda ba mai koyarwa ba – ya tashi tsaye wajen bin ka’idar aiki da ɗabi’a yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa mulkinsa zai gina jami’ar da ake samun shugabanci ne ta hanyar hidima da gaskiya da rikon amana a tsakanin juna.

“Dole ne mu tashi tsaye wajen gina cibiyarmu ta ilimi da ke karfafa guiwa, ya wadda ke neman inganci, kuma ke yaba wa jajircewa a bangarori daban daban" in ji shi.

Post a Comment

0 Comments