ALGON ya ziyarci ɗalubai sakandare da suke zana jarabawar samun tallafi zana Neco da MBais
Daga Idris Umar,Zariya
A ranar Litinin ne shugaban kungiyar ciyamomin jihar Kaduna kuma shugaban karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru ya ziyarci makarantu biyu da suke gudanar da jarabawar tantance duk masu bukatar zana jarabawar Neco da Mbais a ƙaramar hukumar Sabon Gari su kimanin 800 marayu da marasa dama.
Wakilin namu ya tabbatar da cewa shugaban ƙaramar hukumar ne ya dau nauyin jarabawar da za a tantance dalibai masu son ci gaba da karatun shiga jami'a amma basu da hali a ƙalla su 800 daga bangarori da daban daban a faɗin ƙaramar hukumar ta Sabon Gari wanda hakan yasa suke nuna jin daɗinsa game da lamarin musamman iyaye da su kansu yaran da suka sami damar shiga jarabawar tantancewar.
Malam Muhammad shi ya jagoranci jarabawar a ɓanren garin Samaru kuma ya nuna komi ya tafi daidai kamar yadda shugaban karamar hukumar ya tsara anyi jarabawar da babu son kai ba siyasa ba ƙabilanci duk wanda yace za a bashi tallafin ci gaba da karatu da ikon Allah kamar yarda shugaba ƙaramar hukumar ya tsara kuma yara sunso anyi masu gwaji yanzu zasu jira sakamakon jarabawar da akayi masu ne kawai.
Hafsat Muhammad daga garin Samaru na cikin waɗan da suka zana jarabawar da take fira da manema labarai tayi godiya ne ga shi wanda ya dauki nauyin gwajin da akayi masu kuma tayi fatan Allah ya bashi nasara akan duk abin da yake nema.
Wani matashi mai suna Yusha'u Sani daga garin Basawa yana cikin matasan da suka yana jarabawar tantancewar shima godiya yayi tare da yiwa shugaban karamar hukumar ta Sabon Gari fatan Alheri.
An fara jarawar lafiya an gama lafiya.
0 Comments