Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Yayan Jam’iyyar APC Na Karamar Hukumar Makarfi Sun Amince Da Takarar Gwamna Uba Sani A Karo Na Biyu


Yayan Jam’iyyar APC Na Karamar Hukumar Makarfi Sun Amince Da Takarar Gwamna Uba Sani A Karo Na Biyu

Daga Idris Umar,Zariya

Shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar (APC) a karamar hukumar Makarfi sun amince da goyon bayan takarar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Dakta Uba Sani, domin ya tsaya takara a karo na biyu a zaben shekarar 2027. Wannan matsaya ta fito ne daga taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar karkashin jagorancin Dr. Abdulkadir Mu’azu Mayere, Sakataren Gwamnatin Jihar kuma Shugaban Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na APC.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa goyon bayan da suka nuna ga Gwamna Uba Sani ya samo asali ne daga irin salon mulkinsa na sanya kowa da kowa a cikin tafiyar da harkokin gwamnati, ba tare da nuna wariyar kabila ba, da kuma jajircewarsa wajen bunkasa yankunan karkara.

Sun yaba da yadda gwamnan ke aiwatar da manyan ayyukan raya karkara, tare da zuba jari mai yawa a fannin noma da ci gaban dan Adam.

A jawabinsa, Dakta Mayere ya bukaci ’yan jam’iyyar da magoya baya su ci gaba da nuna biyayya da kishin jam’iyya, tare da kara kokari wajen yada nasarorin da gwamnatin Gwamna Uba Sani ta cimma a fadin jihar. Ya kuma tabbatar da cewa karin ayyukan ci gaba masu amfani da jama’a za su ci gaba da gudana a karamar hukumar Makarfi da jihar baki daya.

Post a Comment

0 Comments