DA ƊUMI-ƊUMI: Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya janye batun gudanar da Hawan Sallah ƙarama na wannan shekarar.
Mai martaba sarki Aminu Ado Bayaro yace "Wannan ya biyo bayan shawarwari daga malamai, shugabanni, dakuma duba zaman lafiyar jihar Kano.
Sarki Aminu ya ƙara da cewa hawan sallah ba abune na a mutu ko ayi rai ba. Idan har hakan zai jawo salwantar rayuka ko dukiya, tabbas ya zama dole a haƙura.
Daga ƙarshe yayi kira da al'umma da ayi amfani da wannan lokaci wajen ziyara, da sauran ayyukan addini.
Me zaku ce ?
0 Comments