Wani ƙwayar maganine ( ja da yalo)?
Daga Fatimah Idris
Tetracycline ko kuma da hausa ana kiransa ( ja da yalo) Yana ɗaya daga cikin magungunan damuke kira ANTIBIOTICS DRUGS.
MENENE ANTIBIOTICS DRUGS ???
Antibiotics wasu magungunane dasuke aiki akan kwayar cutar bacteria. Ana amfani dasu yayin da kwayoyin bakteriya suka kawo cuta ko kuma Wani lahani a jikin mu.
NB
Antibiotics Yana aikine iya a kwayoyin bakteriya, Sannan kowanne antibiotics drugs akwai kalar kwayar bakteriya dayake aiki a kanta.
Tetracycline ( ja da yalo) Yana aikine a jikin mu musamman a gurare kamar fata (skin), hanyar iska (Respiratory tract), hanyar fitsari (Urinary tract), hanji (Intestine), da sauransu
AMFANIN TETRACYCLINE ( Ja da yalo)
Ja da yalo ana amfani dashi ne a cututtuka kamar :-
1- Cututtukan da suka shafi fata Wanda kwayar bakteriya suka kawo.
2- Nimoniya ( pneumonia)
3- Zafin fitsari kamar ace Rana.
3- Gyambon ciki ( ulcer).
4- Cututtukan da Ake kamuwa ta hanyar jima'i wato (sexual transmitted infections) kamar gonorrhea, syphilis ko Chlamydia.
5- Amai da gudawa
da sauransu......
MATSALOLIN DA TETRACYCLINE ( Ja da yalo) YAKE HAIFARWA
1- Ƙaiƙayi a fata
2- Numfashi da kyar
3- Gudawa
4- Kumburi a fuskar ko maƙogwaro ko leɓe
5- Amai/ tashin zuciya
da sauransu
MUTANAN DA BAIKAMATA SUYI AMFANI DA TETRACYCLINE ( Ja da yalo) BA
1- Mace Mai ciki, domin zai iya cutar da hantar uwar wato ( hepatotoxicity). ko kuma zai iya shafar haƙorin yaron ta yadda zai sa hakorinsa su canza kala kamar suyi Baƙi ko kuma wata kalar wato discoloration of teeth), sannan kasusuwan yaron bazasu yi karfi ko kuma girma yadda ya kamata bah.
2- Mace Mai shayarwa
3- Yaro ɗan ƙasa da shekara takwas, saboda Yana shafar yanayin girman da yaro zaiyi.
MAGUNGUNAN DA BA' ASHA TARE DA TETRACYCLINE ( Ja da yalo) A LOKACI GUDA
1- Paracetamol
2- Maganin ulcer na ruwa
3- Augmentin
4- Magungunan da suke ɗauke da sinadarin calcium, magnesium, aluminum zinc.
5- Laxative
6- Acetazolamide
ABINCI DA BA'ACI LOKACIN DA ZA'A SHA TETRACYCLINE ( ja da yalo)
1- Madara,ko yoghurt ko nono
2- Tafasa ( senna)
3- Duk abinci Wanda yake dauke da sinadarin calcium, magnesium aluminum ko zinc.
YADDA AKE SHAN TETRACYCLINE ( ja da yalo)
Anfiso asha 1hrs kafin kaci abinci ko kuma 2hrs bayan kaci abinci
SHAWARAR Abnas Kura
A taƙaita yawan amfani da tetracycline (ja da yalo) domin Yana da saurin sabawa da kwayoyin bakteriyar, musamman yin amfani dashi ba yadda yakamata bah, ta yadda Hakan zaisa bazai na iya yin aiki bah.
Kada kasha ja da yalo ba tare da sahalewar malamin asibiti bah.
Pharm tech SHUAIBU JIBRIN
26/3/2025
0 Comments