Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Duk Halitta Musulma Ce, A Imani Aka Bambanta - Shehu Isma'ila Umar Almadda


Duk Halitta Musulma Ce, A Imani Aka Bambanta - Shehu Isma'ila Umar Almadda 

Addinin Musulunci da ke nufin mika wuya da sallama wa Allah Ta’ala ya hada kowa da kowa duk halitta, sai dai a wurin imani ne aka bambanta. Haka nan addinin na musulunci wanda ya taho tun daga zamanin Annabi Nuhu (AS) har zuwa kan Annabi Muhammad SAW ɗaya ne, amma ana samun bambanci ne ta fuskar tsarin Ibadar da kowa al’ummomi ke yi. 

Shehu Isma'ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya bayyana hakan ne a yayin da yake ci gaba da karatun Tafsirin Alƙur’ani mai girma a rana ta 28, a Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group da ke cikin birnin Kaduna.

A ci gaba da karatun, Almadda ya ce, yarda ko sallama wa Ubangiji tana kan mataki uku, na farko shi ne Matakin Halitta, da ya kunshi imani da Allah, da ranar Alkiyama. Sai na biyu Matakin Ɗan Adam mai hankali, wanda ya haɗa da sallamawa irin ta matakin halitta sannan kuma da aiki mai kyau. Na uku shi ne Matakin aiki Ibada, inda shi kuma ya tattaro muminai kaɗai mabiya manzanni, da suka haɗa da Annabi (SAW), Annabi Isa (AS), Annabi Musa (AS), Annabi Ibrahim (AS) da dai sauran manzanni annabawa.

Shehu Mai Diwani ya ce, duba da haka, za a iya fahimtar cewa, ba mabiya Addinin Annabi Muhammad (SAW) ne kaɗai Musulmai ba, hatta Fir'auna ya ce shi ma Musulmi ne, sai dai Ubangiji ya ce "maɓarnaci" ne amma Allah bai ce ba ya cikin Musulmai ba.

Shehun Malamin wanda ya kawo ayoyin Alkur’ani mai girma da suka nuna musuluncin duk halitta a matakin Islam, da imani da kuma ihsani da yadda Annabawa suka bayyana kawunansu a matsayin musulmai, har ila yau ya ce, Addinin Allah ya ƙunshi abubuwa masu yawa da suka hada da:  
-Kyawawan Ɗabi'u 
-Dokoki na Shari’a kamar rabon gado ko Wasiyya
-Kafa dangi ko Iyali kamar Aure ko rabuwarsa
-Uƙuba, kamar haddi wanda ƙarshensa Kisa ko a sassauta ya zama daurin rai-da-rai
-Shirin zaman lafiya da yaƙi
-Riba, don kiyaye tsarin kasuwanci 

Ya kara da cewa, duk wadanda ba wannan ba, tsarin mulki na zamantakewar al’umma ko kasa (Constitution) zai tsara shi.

Shehu Isma’ila Almadda, ya yi kira ga masu yawaita kafirta musulmi da su ji tsoron Allah su daina, yana mai cewar tun daga zamanin Annabi (SAW) idan za a yi maganar wadanda suka yi imani da shi “Musulmai Muminai” ake kiransu amma da sabani na siyasa ya yi tsamari sannu a hankali aka mayar da sunan ya zama “Musulmai” kawai don tsaurarawa.
Ya kara da cewa, wannan yanayi da aka shiga ne ya haifar da hatta a cikin Musulman aka rika samun masu yawaita kafirta musulmi da shafa wa wasu bakin fenti da jefa al’ummar Annabi (SAW) a wuta saboda son rai kawai ko sabanin siyasa.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi mu dawo kan fidira ta halittar Allah da turbar da Manzon Allah (SAW) ya dora al’umma a kai, da guje wa bata wa Allah halittarsa ta hanyar nuna kyawawan dabi’u kamar yadda aka gani daga Annabi (SAW) a zamantakewarsa ta birni da ya kafa a Madina.

Post a Comment

0 Comments