Shugaban ƙungiyar Hezbollah Sheikh Naim Qassem, ya yi watsi da tsawaita wa'adin da Isra'ila ta yi na ficewa daga kudancin Lebanon, yana mai cewa hakan bai dace ba.
"Wa'adin yarjejeniyar ya ƙare ranar Lahadi, kuma babu wani dalili na wani ƙarin wa'adi," in ji shi, yana zargin Isra'ila da keta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta sau 1,350.
Qassem ya yi nuni da cewa, ƙungiyar Hezbollah ta ƙauracewa ɗaukar fansa duk da keta sharuɗan yarjejeniya da ake yi, bisa la'akari da buƙatar mahukuntan Lebanon ta yin hakuri.
A cewar ma'aikatar lafiya ta Labanon, sojojin Isra'ila sun kashe aƙalla mutane 24 tare da jikkata wasu aƙalla 141 a kudancin Lebanon a ranakun Lahadi da Litinin, yayin da dubban mutane suka yi yunƙurin komawa gidajensu.
"Duk wani sakamakon jinkirin janyewar zai kasance alhakin Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da Faransa da Isra'ila," in ji Qassem, ya ƙara da cewa "ƙungiyar" tana da 'yancin yin abin da ta ga ya dace don mayar da martani ga "Isra’ila".
0 Comments