An kaddamar da ginin bubban masallacin kofar fadar Sarkin Zazzau dake Zariya Wanda ya rutta watanin baya da suka wuce kuma yayi sanadiyyar rasuwar mutane a lokacin shi dai wannan bubban Masallacin na kasar Zazzau na Sarkin Zazzau Abdulkarimne kuma ya rufta ana tsaka da sallah La'asarne sakamakon ruwan sama mai karfin gaske. Wannan masallaci yana da tarihi sosai.
Wannan masallacin tsohon magininanne kuma shahararre wato mai suna Bubban Gwani ya ginashi tun shekaru kusan dari Biyu da suka wuce.
Bisa wancan lalura da ta farune masarautar kasar Zazzau bisa jagorancin mai Martaban Sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli ta dau alwashin rusheshi tsohon ginin don sake saban wani ginin a wannan muhalli.
A yau 15/12/2024 masarautar ta kaddamar da bukin aza harsashi ginin Sabon masallacin tare da karbar gudummawa daga wasu manyan mutane
Daga cikin Mayan mutane da suka hallaci taron akawai Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani da kakakin majalisar taraiyya RT honorable Abas Tajuddin da ministan muhalli Alhaji Balarabe Lawal Abas.
An kaddamar da ginin masallacin Lafiya an tashi lafiya.
0 Comments