Header Ads Widget

Responsive Advertisement

An kaddamar da ginin bubban masallacin kofar fadar Sarkin Zazzau dake Zariya


An kaddamar da ginin bubban masallacin kofar fadar  Sarkin Zazzau dake Zariya Wanda ya rutta watanin baya da suka wuce kuma yayi sanadiyyar rasuwar mutane a lokacin shi dai wannan bubban Masallacin na kasar Zazzau na Sarkin Zazzau Abdulkarimne kuma ya rufta ana tsaka da sallah La'asarne sakamakon ruwan sama mai karfin  gaske. Wannan masallaci yana da tarihi sosai.

Wannan masallacin tsohon  magininanne kuma shahararre wato mai suna Bubban Gwani ya ginashi tun shekaru  kusan dari Biyu da suka wuce.

Bisa wancan lalura da ta farune masarautar kasar Zazzau bisa  jagorancin mai Martaban Sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli ta dau  alwashin rusheshi tsohon  ginin don sake saban  wani  ginin a wannan muhalli.

A yau 15/12/2024 masarautar ta kaddamar da bukin aza harsashi ginin Sabon masallacin tare da karbar gudummawa daga wasu  manyan  mutane

Daga  cikin Mayan mutane da suka hallaci taron akawai Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani da kakakin majalisar taraiyya RT honorable Abas Tajuddin da ministan muhalli Alhaji Balarabe Lawal Abas.

An kaddamar da ginin  masallacin Lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments