Albania ya tabba shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari
Daga Idris Umar Zariya
A ranar 4/11/2024 Shiek Honorable Abubakar Albani ya hau kujerar karagar mulkin ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna .
Kafin shigansa Ofishin nasa da ƙwana ɗaya ne sheik Albani yayi abin burgewa da babu wani shugaban ƙaramar hukumar daya taɓa yinsa wanda hakan ya janyo hankalin al'ummar ƙaramar hukumar ta Sabon Garin da jihar Kaduna baki ɗaya.
Daga cikin abubuwan da shi Honorable Albani yayi da ya baiwa jama'a sha'awa shine, a karon farko a ranar jajiberin shigansa offis ya gaiyyato dukkan masu ruwa da tsaki kuma masu faɗa aji a bangaren siyasa da kuma ɓangaren kungiyoyin addinai har da sarakunan dake fadin ƙaramar hukumar ta sabon Gari da jihar Kaduna gudanar da taron wa'azi ga juna a matakin farko wanda babu wani shugaban ƙaramar hukumar daya taɓa yin hakan tunda aka samar da karamar hukumar Sabon Garin.
Wannan sabon salon da sabon shugaban ya bullo da shi ya burge jama'a sosai a matsayin sa na gogaggen ɗan Ahalissu ɗan Izala na gidi amma ya gayyaci dukkan bangarorin Addini don neman ci gaban ƙaramar hukumarsa wannan abu ja'ma'a sun yaba da lamarin kuma hakan ya nuna zai fitar da Jambiyar APC da gwamna jihar kaduna kunya a idon duniya musamman abokan adawarsa.
Wakilinmu ya nakalto mana cewa, taron da shi Honorable Albani ya kira kuma ya haɗa a wannann rana kafin shigarsa offis ya tara dubban jama'a da babu wanda baiyi mamakin hakanba.
Yace, taron an kirashine ne don tunatar da juna da taya juna murna musamman Al'ummar ƙaramar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki ɗaya.
Taron an gudanar da shine a harabar sakateriyar karamar hukumar ta Sabin Gari kuma ya sami karɓuwa sosai ta bangaren kungiyoyin addinai da shuwagabaninsu har sarakuna da masu anguwanni.
Daga cikinsu akwai kungiyar JIBWIS Kaduna da Jos akwai Kungiyar Munazzamatul Islam reshen ƙaramar Hukumar Sabon Gari da jiha baki ɗaya sai kungiyar CAN suma sun zo da cibiyoyin tsaro da kungiyoyin masu zaman kansu duk sun halacci wannan waje don amsa gaiyyatar da akayi masu kuma sun nuna jin daɗi da wannan ƙokari na Honorable Albani Samaru ya kawo a yayin da ake zantawa dasu.
Bincike ya nuna cewa Honorabul Abubakar Jamil Albani ya canza tarihin siyasar karamar hukumar sabon Gari baki ɗaya wajan samar da hadin kai a cikin al'Umar ƙaramar hukumar Sbon Gari baki ɗaya musamman ganin irin jama'ar da ya tara a matakin Farko.
Wani abin burgewa shine yadda dukkan manyan mutanen da suka gabatar da jawabi a wannann taro sukai ta nuna yabo tare da yi masa addu'o'i na samun nasara .
Daga cikin manyan baki akwai kakakin majalisar jihar Kaduna Rt Honorabul Yusuf Liman sai mai girma Madarkin Zazzau Alhaji Munnir Jafaru da Honorable Garba Datti Babawo Sharif Dallami Muciya da dai sauran manyan malamai.
Yayi jawabinsa Ƙaƙakin Majalisar jihar Kaduna Rt Honorabul Yusuf Liman yayi kirane ga sabon shugaban da yaji tsoron Allah yayin da yake gudanar da shugabancinsa kuma yayi fatan al'ummar karamar hukumar Sabon Gari zasu bashi goyon baya, kuma kakakin yayi godiya bisa yadda akaba APC goyon baya .
A nasa jawabin yayi kammala taron Sheikh Albani yayi godiya ga dukkan kungiyoyin Addinai da suka zo musamman shugabanninsu da suka amsa gaiyatarsa Albani yayi rokon ci gaba da bashi goyon baya tare da addu'a da shawararwari, kuma yayi fatan yadda kowa yazo lafiya Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya .
An fara lafiya an tashi lafiya
0 Comments