Ƙiba ko teɓa jibgaggen kitse ne a sassan jiki. Galiban kitse na fara jibgewa a sassan jiki idan mutum yana cin abinci fiye da buƙatar jikinsa. Bayan jiki ya yi amfani da iya abin da yake buƙata, sai jiki ya sarrafa ragowar abincin da jiki ba ya buƙata zuwa kitse sannan a jibge shi a sassan jiki musamman a ciki, kayan ciki, tsokoki da sauran sassan jiki. Mutum zai ɗinga ƙone kitse gwargwadon motsa jiki ko atisayen da yake yi kullum.
Jibgaggen kitse fiye da kaso 10 cikin 100 (10%) na nauyin jiki ba shi da amfani ga jiki face dakon barazana ga lafiyar jiki.
Ƙiba ko teɓa na da koma-baya kamar:
1. Munana sifar jiki
2. Raguwar kuzari ko karsashi
3. Matsalolin bacci
4. Matsalolin saduwa da iyali
5. Dakushewar kaifin ƙwaƙwalwa
Barazana ga lafiyar sassan jiki kamar:
1. Hanta
2. Zuciya
3. Ƙoda
Haɗarin janyo lalurori kamar:
1. Hawan jini
2. Ciwon siga
3. Ciwon zuciya
4. Ciwon daji (kansa)
5. Ciwon baya
6. Ciwon amosanin gwiwa
Kasancewa cikin matsakaicin nauyin jiki ta hanyar samar da daidaito tsakanin cimaka da motsa jiki shi ne mafita.
© Physiotherapy Hausa
0 Comments